Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a ranar Talata a Owo-Ijo dake wani sashe na babban titin Lagos zuwa Ibadan ya rutsa da mutane da dama.
A cewar wani shedar gani da ido wata babbar mota dake É—auke da kwanon rufi ta samu matsalar shanyewar birki inda ta ci karo da wasu motoci uku.
Hakan ya sa motar ta kwace abun da ya kai ga faruwar hatsarin.
Kawo yanzu babu wata sanarwa da hukumomi suka fito kan yawan mutanen da suka jikkata a hatsarin.
Hatsuran mota da suke haɗawa da manyan motoci abu ne da ya zama ruwan dare akan manya da ƙananan titunan ƙasarnan.