Hare-hare sun yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da dubu cikin wata 4

Wata kungiya mai zaman kanta da ke mai da hankali kan kare hakkin dan Adam da samar da zaman lafiya, Stefanos Foundation, ta bayyana cewa tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu, 2023, an kai hare-hare 217 a jihohi 34 na Najeriya.

A cewar kungiyar kare hakkin bil’adaman da ke Jos, hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane 1,872, an yi garkuwa da mutane 714, sannan mutane 65 sun samu raunuka daban-daban.

Ms. Fatima Njoku, Manajar wani sashe a gidauniyar Stefanos, a yayin wata ganawa da manema labarai na hadin gwiwa a Abuja ranar Alhamis, ta jaddada cewa akwai bukatar a dauki matakin gaggawa don magance musabbabin tashe-tashen hankula a sassan kasar nan.

Ta ce, “Daga rahotannin gani da ido kuma shaidar wadanda abin ya shafa kai tsaye, muna iya cewa ana kai hare-haren ne a zahiri iri ɗaya, tare da maharan sanye tufafi iri ɗaya cikin salo daya.”

“Hakan ya faru ne a Agatu, Guma, Logo a jihar Benue, Kagoro, Zangon Kataf, Kajuru, Kafanchan a kudancin Kaduna, Bassa, Riyom, Barkin Ladi, yanzu Mangu a jihar Filato, kuma ana ci gaba da jerin gwano”.

More News

Sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan ta’adda 191 tare da kama 184

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana hakan ne a wata sanarwa wacce aka fitar bayan wani taron manema labarai da rundunar ta yi a Abuja...

Farashin gangar ɗanyen man fetur ya ƙaru zuwa $97

Farashin ɗanyen man fetur ya karu sosai a ranar Alhamis inda aka rika sayar da kowacce ganga kan dalar Amurka $97. Farashin man nau'in Brent...

Kungiyar ƙwadago ta NLC ta dage kan tsunduma yajin aiki

Kungiyar ƙwadago ta NLC ta ce babu wata yarjejeniya da ta shiga da gwamnatin tarayya domin ta dakatar da shiga yajin aikin sai baba...

Wani wanda ya gama jami’a ya yi yunkurin kashe kansa saboda rashin ba shi satifiket ɗinsa

Wani wanda ya kammala karatun digiri a jami’ar Ambrose Ali da ke Ekpoma a jihar Edo mai suna Precious Ogbeide ya yi yunkurin kashe...