Har yanzu Sanusi ne sarkin Kano—Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce hukuncin da wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ta yanke a safiyar ranar Alhamis ya nuna cewa har yanzu Alhaji Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano.

Babban Lauyan jihar kuma kwamishinan shari’a Barista Haruna Isah Dederi ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnati da yammacin Alhamis.

More from this stream

Recomended