Har yanzu babu sauyi a Old Trafford, inji Mourinho

Jose Mourinho

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jose Mourinho ya ci kofin Europa a Manchester United

Jose Mourinho ya yi magana game da halin da Manchester United ta tsinci kanta a farkon Premier bana, kuma ya yi imanin cewa babu wani ci gaba da ta samu tun bayan tafiyarsa.

Ole Gunnar Solskjaer ya karbi aikin Man United daga hannun Mourinho a kakar wasannin da ta gabata kuma dan kasar Portugal din ya tuna lokacinsa a Old Trafford.

“Ba mu da kyau a kakar da ta gabata amma ni ban ga wani ci gaba ba a yanzu duk da zuwan sababbin ‘yan wasa guda uku, ‘yan wasa masu hazaka,” Mournho ya fada sanda ya bayyana a gidan talabijin na Sky.

“Suna shigo da zakakuran ‘yan wasa, sai dai kungiyar a matsayinta na kulob ne ni ba ta yi mani ba.

“An kore ni, babu mamaki na cancanci a kore ni din tunda ni ne koci. Sai dai abin haushin shi ne har yanzu ba su canza ba.

“Mutane suna tunanin ina jin dadin abin da yake faruwa, ba na jin dadi kwatakwata.”

Tsohon kocin Real Madrid da Chelsea da Inter Milan din ya yi hasashen cewa Manchester United za ta kare a tasakanin mataki na hudu zuwa na shida.

  • Akwai jan-aiki a gabanmu a La Ligar bana – Suarez
  • Liverpool ta ci gaba da jan zarenta a Premier

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...