Hadakar Kungiyoyin Kudancin Najeriya Na Kira Ga Fulani

Hadakar kungiyoyin Yarbawa, yankin Naija Delta, da ta jama’ar tsakiyar Najeriya ta Afenifere, da ta Kudancin kasar sun maida martani.

Kungiyoyin sun maida martani ne game da kiran da wata kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya tayi cewa, Fulani makiyaya dake zaune a yankin kudancin kasar su dawo Arewa.

Sanarwar wanda shugabannin kungiyoyin irin su Cif Ayo Adebanjo na afenefere dana Chaneze Ndigbo Cif Nnia Nwodo, da Edwin Clark na Naija Delta, suka rattabawa hannun, sunyi Allah wadai da kiran da kungiyar Dattawan Arewa karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi tayi na Fulani su koma yankin Arewa domin rayukan su na cikin hatsari.

Koda yake wakilin Muryar Amurka bai samu jin tabakin shugabannin na Afenefere game da wannan sanarwa ba, sarakunan Yarbawa sunyi kira ga Fuani dake wannan yanki da suyi watsi da kiran na barin yankin, su kuma cigaba da gudanar da kiwon dabbobin su, domin tabbatar da zaman lafiya, kamar yadda daya daga cikin sarakunan yarbawa maimartaba Oba Ahmed Adekunle Oyelude ya shaida.

Domin jin tabakin sauran al’ummar yanki dana Arewa, wasu sun ce cece kuce tsakanin kungiyoyin yankin na Arewacin Najeriya da kuma takwarorinsu na Kudanci ko Yanmancin kasar, ya fito ne bayan wani matakin gwamnatin Muhammadu Buhari tace, zata kafa Rugage a yankunan kasar ciki harda Kudu.

Koda yake daga baya ta soke shirin, gwamnati ta fitar da sanarwar ta hannun kakakin fadar shugaban kasa, Malam Garba Shehu inda tayi kira ga Fulanin dake zaune a kudancin Najeriya da suyi watsi da wannan kira da shugaban kungiyar Dattawan Arewacin kasar, farfesa Ango Abdullahi yayi.

Suma ‘yan jam’iyar APC mai mulki a Legas sunyi tsokaci akan wannan al’amarin, kamar yadda daya daga cikin shugaba Alhaji Ado Dansudu yayi bayani.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...