‘Gyara matatun man Najeriya zai ba da kafar cin hanci’

Port Harcourt is Nigeria's oldest oil refinery built in 1965.

Asalin hoton, AFP

Masana na ci gaba da tsokaci kan kwangilar da gwamnatin Najeriya ta bayar ta gyara daya daga cikin manyan matatun manta wadda ke birnin Fatakwal a kudancin kasar a kan kudi dala biliyan daya da miliyan dari biyar.

Gwamnatin ƙasar ta ba da kwangilar ne ga kamfanin Tecnimont mai hedikwata a Italiya.

Duk da cewa Najeriya na daya daga cikin kasashe mafiya arzikin mai a duniya, to amma takan sayo tataccen mai ne daga kasashen waje saboda lalacewar matatunta – kuma ana zargin lamarin na haifar da rashawa da tsadar man ga gwamnati da kuma ‘yan kasar.

Dokta Ahmed Adamu, masanin tattalin arzikin man fetur a Najeriya ya shaida wa BBC cewa matakin gwamnatin sam ba zai haifar da wani ci gaba ba ganin yadda shekarun baya ma aka dauki irin wannan matakin amma kuma ba a ga wani abin a zo a gani ba.

A cewarsa, yunƙurin gyara matatun man bai zama dole ba saboda akwai mahimman abubuwa da ya kamata a ce gwamnatin ta mayar da hankali a kai domin ci gaban Najeriya.

“A wannan lokaci da duniya ta karkata aÆ™alarta ta hanyar gwamnati ta cire hannunta a harkar kula da man fetur, sai muka ga Najeriya yanzu ma take Æ™ara dulmiyar da hannunta a cikin kula da harkar man fetur”. in ji masanin.

Dokta Ahmed Adamu ya bayyana cewa zai yi wuya a iya kammala aikin cikin lokacin da aka É—iba na gudanar da shi.

Ya bayyana cewa yawan gyara tsofaffin matatun man “wata dama ce ga wasu suke amfani da ita domin samun kuÉ—in shiga ko kuma a yi cin hanci da rashawa”.

Yadda aikin gyara matatar man zai amfani Najeriya

A cewar masanin tattalin arzikin man fetur ɗin, matatar man ta Fatakwal, idan za ta yi aiki ɗari bisa ɗari, za ta iya biyan rabin buƙatun man da ƴan Najeriya suke da shi.

Sai dai ya É—iga ayar tambaya kan yiwuwar ita matatar man ta yi aiki É—ari bisa É—ari ganin cewa tsohuwar matatar mai ce.

Ya kuma ce ko da an gyara matatar man dole ne sai an shigo da man daga wasu Æ™asashen amma a ganinsa, gyara matatar zai yi tasiri sosai wajen samar da mai cikin sauÆ™i a Najeriya tare da rage hauhawar farashin kayan masarufi saboda “mai yana alaÆ™anta da sauran farashin kayan abubuwa”.

—BBC Hausa

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...