
Zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya karbi bakuncin gwamnonin PDP a gidan gwamnati na Defense House dake Abuja.
Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde sun gana da shugaban kasar mai jiran gado.
Gwamnonin biyu na jam’iyyar PDP na daga cikin mambobin kungiyar G-5 da suka ki yarda su marawa Atiku Abubakar baya a zaɓen shugaban kasa na 2023.
Wata majiya dake kusa da zaɓaɓɓen shugaban kasar ta tabbatarwa da jaridar Daily Trust cewa gwamnonin sun gana a ranar Juma’a da daddare amma ganawar ta su bata da alaƙa da siyasa.