Gwamnatin Tarayya Na Tallafawa ‘Yan Kasuwa A Jihar Kebbi

0

VOA Hausa
A jihar Kebbi dake arewa Maso yammacin kasar ‘Yan kasuwa ne suke murnar samun bashin naira biliyan biyu domin farfadowa da kasuwancin su.
“Yan kasuwa dari biyar da arba’in da shida ne suka amfana da samun bashin kudi daga naira miliyan daya zuwa biyar karkashin shirin bayar da bashin ta hukumar Nirsal domin farfadowa da sana’o’in su da suka tabarbare sanadiyar cutar murar mashako.
Babban lauyan gwamnati kuma Ministan Shara’a na Najeriya Abubakar Malami ya ce domin saukaka samar da bashin ga jama’ar, wata kungiya dake fafatukar samar da ci gaban al’umma ta Hadimiya ita ce ta shiga gaba wajen nemo wadannan kudade ga mutanen.
Ya ce “gwamnatin tarayya tana sane da matsalolin da ‘yan kasuwa suka fada ciki sanadiyar annobar coronavirus, dalilin haka ne kuma take aiki tare da wannan kungiya ta Hadimiya domin ci gaba da tallafawa al’umma.
Ko bayan wannan, ministan ya ce bisa ga saukaka matsalar rashin samun ruwa ga jama’a kungiyar tayi fafatukar samar da riyojin burtsaste 150 a sassa daban daban na jihar ta Kebbi.
Faruk Abubakar Mai Sudan shine sakataren kungiyar Hadimiya ya ce wannan aikin kamar soman tabi ne daga shirin da take da shi na samar da ci gaban rayuwar al’ummar jihar Kebbi.
Duba da cewa akwai masu na neman irin wannan tallafin bashi da yawa da basu same sa ba, wadanda suka amfana da samun bashin ta hanyar wannan kungiyar sun bayyana farin cikin su..
Da yake an rarraba takardun amincewar bayar da bashin ga mutanen abin jira a gani shine shigowar kudin da kuma yadda zasu yi amfani da su wajen habaka kasuwancin su duk da yake cutar murar mashako karo na biyu na barazana ga jama’a a kasashen duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here