Gwamnatin Kano ta janye dokar ta kaita zirga-zirga

Gwamnatin jihar Kano ta janye dokar taÆ™aita zirga-zirga da aka saka a jihar biyo bayan É“arna da sace dukiyar gwamnati da ta jama’a da aka yi a  lokacin da aka gudanar zanga-zanga kan halin matsin rayuwa da al’umma suke ciki.

Kwamishinan yaÉ—a labarai na jihar, Baba Halilu ÆŠantiye shi ne ya sanar da janye takaita zirga-zirgar a cikin wani jawabi da aka watsa a kafafen yaÉ—a labarai a ranar Litinin.

A ranar 1 ga watan Agusta ne gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sanar da saka dokar hana fita ta tsawon awanni 24 biyo bayan É“arnar da aka yi a lokacin zanga-zangar.

A ranar 2 ga watan Agusta gwamnan ya sassauta dokar da awanni biyar domin bawa mutane damar gudanar da sallar Juma’a.

Kwamishinan ya ce gwamnan ya janye dokar bayan da ya gamsu cewa sha’anin tsaro ya inganta a jihar.

Ya ƙara da cewa yanzu mutane za su iya cigaba da gudanar harkokinsu na yau da kullum a cikin doka da oda.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen É—an bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen É—an bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka Æ´anbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...