Gwamnatin Bauchi ta gano ma’aikatan bogi

Bala Muhammad
Image caption

Gwamnatin jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya na ci gaba da shan suka kan kin biyan albashin ma’aikata da ‘yan fansho fiye da 4i,000, bisa zargin cewa su na boge ne.

Adadin mutanen ya kai fiye da kashi 40% na illahirin ma’aikata da ‘yan fansho a jihar.

Gwamnatin jihar ta ce an gano sunayen wadannan mutanen ne a cikin kundin bayanan masu karbar albashi da fansho duk da cewa ba su da lambar Tantance Asusun Banki ta BVN don haka ake da shakku kan sahihancin kasancewarsu ma’aikata ko ‘yan fansho.

To sai dai wasu daga cikin ma’aikatan na cewa suna da wannan lamba, kuma su ma’aikata ne na gaskiya. Daya daga cikinsu da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa su na cikin mawuyacin hali.

”Yace kashi 70% cikinmu ga albashi muka dogara daman da albashin ake hidimadar iyalai, ga bashin da ma’aikata suka ci. Ina da mata uku da ‘ya’ya 13, kudin da zan biya na makarantar yara ma ba a samu ba.

An ce muna da matsala da BVN amma na san na yi hatta katin shaida ina da shi, amma sai gashi suna na ya fito a cikin wadanda aka fitar a matsayin ma’aikatan bogi.

kusan shekara 20 kenan ina aikin gwamnati dan haka batun ba ma’aikacin gwamnati ba ne bai taso ba. Babban abin damuwar shi ne ba mu san matsayinmu ba, saboda yadda aka manna sunayenmu har yanzu ba mu san yaushe za a tantance mu ba, dan haka muka ci gaba da zuwa aiki amma dai za mu kashe kudin motar zuwa gashi albashi bai samu ba.”

To sai dai kakakin Gwammnan jihar ta Bauchi Alhaji Mukhtar Muhammad Gidado ya shaida wa BBC cewa da zarar gwamnatin jihar ta kammala bincike za a biya wadanda aka tabbatar da sahihancin kasancewarsu ma’aikata ko ‘yan fansho.

Ya kara da cewa ”Gwamnatin jihar ta dakatar da dukkan sakatarori da ma’aji na hukumar ilimi matakin farko SUBEB na kanana hukumomi 20, da shugabannin sassan lafiya na kananan hukumomi 20 an bukaci su sauka daga kujerunsu.

An dakatar da su dan a yi bincike mai inganci, saboda karkashin jagorancinsu ne aka samu wannan lamari, sannan gwamna Bala Muhammad ya kafa wani kwamiti dan yin binciken kuma karkashin jagorancin tsohon shugaban ma’aikata na jihar Bauchi Alhaji Adamu Ibrahim Gumba an ba su makwanni biyu su kammala bincike.

Kuma gwamnati ba ta kori kowa daga bakin aiki ba sannan albashinsu na watan Nuwamba an adana shi a wani asusu na musamman da zarar an kammala bincike duk wanda aka tantance aka samu ya na da BVN za a biya shi albashinsa ba tare da lokaci ba.”

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...