
Umo Eno, gwamnan jihar Akwa Ibom ya sanar da sauya sheka daga jam’iyar PDP ya zuwa jam’iyar APC.
Da yake magana ranar Juma’a a Uyo babban birnin jihar Eno ya ce sauya shekar ne bayan da ya dauki tsawon watanni uku yana tattaunawa da wasu manyan masu ruwa da tsaki a jihar.
Gwamnan ya ce an dauki tsawon lokaci a fagen siyasar jihar da kuma Najeriya ana tattauna batun fitarsa daga jam’iyar PDP wacce ta bashi damar cimma gagarumar nasara a siyasarsa har ya zama gwamnan jihar.
Eno ya ce ya mika takardar ficewarsa daga jam’iyar PDP ga shugabannin mazaba da kuma kwafin takardar ga shugabannin jiha da na kasa .
Ya godewa jam’iyar PDP kan goyon baya da ta bashi na tsawon shekaru 2 da ya shafe akan mulki.