
Guguwa mai karfi ta lalata gidaje da dukiya ta miliyoyin naira a unguwannin Nayi Nawa da Pawari a karamar hukumar Damaturu ta jihar Yobe.
Bala’in guguwar ya raba daruruwan mutane da gidajensu.
Wata dake zaune a ɗaya daga cikin inda abin ya faru ta bayyana cewa guguwar ta lalata gidansu lokacin da suke bacci da misalin karfe 3 na dare.
A cewar ta da yawa daga cikin wanda abin ya shafa suna cikin mawuyacin hali inda tayi kira ga gwamnati da kuma gwamnati da ta kawo musu ɗauki.