Giwaye shida sun mutu a kokarin ceto junansu | BBC Hausa

Daya daga cikin giwayen da ya tsira yana kokarin tashin dan uwansa da ya mutu

Hakkin mallakar hoto
KHAO YAI NATIONAL PARK

Image caption

Daya daga cikin giwayen da ya tsira yana kokarin tashin dan uwansa da ya mutu

Wasu giwaye shida sun mutu a kokarin ceto junansu a wata makwararar ruwa da ke Thailand.

Jami’ai a kasar sun shaida cewa lamarin ya faru ne yayin da wani dan jinjirin giwa ya hau har can kololuwar makwararar ruwan, hakan ya jawo ya zame kasa.

Lamarin ya faru ne a wata makwararar ruwa da ke wurin yawon bude ido na Khao Yai da ke kasar.

An hango wasu giwayen guda biyu a can kololuwar dutse daga gefe suna niyyar fadawa cikin ruwa inda daga baya jami’a suka kora su.

Wannan makwararar ruwan na da dumbin tarihi, kuma an shaida cewa irin wannan lamarin ya taba faruwa a can baya.

Hakkin mallakar hoto
THAILAND DNP

Giwaye takwas sun taba fadowa daga saman makwararar a 1992, wanda hakan ya ja hankalin duniya.

Ma’aikatar kula da wuraren yawon bude ido da namun daji da dazuka ta Thailand ta shaida cewa an kira jami’a a ranar Asabar da misalin karfe uku na dare, kusan takwas na dare kenan agogon GMT, kan cewa wasu giwaye sun yi tsaye sun yi cirko-cirko a kololuwar makwararar ruwa.

Bayan sa’o’i uku, sai kawai aka ga gawar jinjirin giwa cikin ruwa a kasa tare da gawarwakin manyan giwaye biyar a gefe.

Hakkin mallakar hoto
THAILAND DNP

Mista Khanchit Srinoppawan ya shaida wa BBC cewa ana nan an sa ido ga sauran giwayen biyu da suka yi kokarin fadawa amma jami’ai suka kora su.

Edwin Wiek wanda ya kirkiri wata kungiya ta namun dawa a Thailand ya shaida cewa sauran giwayen da suka rage zai yi wuya su rayu sakamakon giwaye na dogara da juna ne domin kare kawunansu da kuma neman abinci.

Lamarin kuma kan iya harzuka su sakamakon giwaye na iya nuna bacin ransu a fili.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...