Ganduje ya zama sabon shugaban jam’iyar APC

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya zama sabon shugaban jam’iyar APC na ƙasa.

An zabi Ganduje a matsayin sabon shugaban jam’iyar ne a wurin taron kwamitin gudanawar jam’iyar da ya gudana a birnin tarayya Abuja.

Har ila yau an zabi Ajibola Basiru daga jihar Osun a matsayin sakataren jam’iyar na kasa.

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima na daga cikin waɗanda suka halarci taron.

More from this stream

Recomended