Babbar Jam’iyyar adawa a Kano ta PDP ta nuna damuwa kan yadda gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya ke neman yi wa asusun jihar karkaf.
Wannan kuwa ya biyo bayan sanarwar da ya yi cewa zai kashe naira miliyan 500 domin ƙawata gadar Ƙofar Ruwa da aka sanya wa sunan marigayi Galadiman Kano Tijjani Hashim.
Cikin wata sanarwa da shugaban PDP Shehu Wada Sagagi ya fitar ta ce, kudin da aka amince a kashe ya yi yawa, kawai ana son a ɓarnatar da dukiyar al’umma ne.
An gano cewa an fara aikin ne makonni gabanin a amince da kashe kudin kuma baya cikin kashe-kashen kudin da aka tsara yi a 2022 ballantana 2021.
“Wannan laifi ne da zai iya janyo mutum ya bar ofishinsa,bin damuwa ne matuka da ya kamata a sanya wa ido da a ce jihar Kano tana da jajirtattun ‘yan majalisar dokoki.
“Muna kira ga kungiyoyin fararen hula da hukumomin hana cin hanci da rashawa irinsu EFCC da ICPC su sanya ido domin tabbatar da bin diddigi da zai tabbatar da kyakkyawan shugabanci.”
Sanarwar ta kara da cewa, “wannan ya nuna ƙarara cewa gwamna na kashe kudaden ba tare da wani ƙaidi ba, wanda hakan zai iya janyo taɓarɓarewar tattalin arzikin jihar gabanin karewar wa’adinsa na biyu, ya kuma yi wa asusun jihar ƙarƙaf.”