Fursunoni 153 sun tsere daga gidan yarin Koton Karfe

Prisoners

Hukumar kula da gidajen yari a jihar Kogi a Najeriya, ta ce tuni ta samu zarafin cafke fursunoni 31 daga cikin 153 da suka tsere daga gidan yarin garin Koton Karfe na jihar Kogi.

Da misalin karfe 5:00 na safiyar ranar Litinin ne dai fursunonin suka tsinke bayan da ruwa kamar da bakin kwarya ya rusa wani bangare na ginin gidan yarin.

To sai dai mai magana da yawun hukumar, DSP Williams Obe Aya, ya shaida wa BBC cewa bayan tserewar fursunonin ne hukumar ta nemi daukin wasu hukumomi da ‘yan banga domin shawo kan fusrsunonin.

DSP Williams ya kara da cewa kawo yanzu jami’an nasu bisa hadin gwiwar ‘yan sintiri sun samu nasarar cafke mutum 31, kuma tuni aka mayar da su gidan yarin.

Sai dai ya ce jami’an nasu na ci gaba da farautar ragowar fursunoni 122 wadanda suka bazama daji.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...