Fitaccen malamin Musulunci ya kafa jam’iyyar hamayya a Mali | BBC Hausa

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ibrahim Boubacar Keita ya kama mulki a watan Satumba na 2013, tare da alkawarin hada kan kasar bayan rikice-rikice daban-daban.

An samu gagarumin gangami na jama’a da suka halarci taron kaddamar da wata sabuwar jam’iyyar siyasa da wani fitaccen malamin addinin Musulunci, Mahamoud Dicko, ya kafa a Bamako, babban birnin kasar Mali.

Sheik Mahamoud ya dauki wannan mataki ne na shiga fagen siyasar kasar a yayin da jama’a ke komowa daga rakiyar gwamnati a sakamakon tabarbarewar tsaro a kasar ta Mali.

Malamin wanda sananne ne a Mali, shekara goma yana jagorancin majalisar harkokin addinin Musulunci ta kasar.

A yayin kaddamar da sabuwar jam’iyyar, Mahamoud Dicko , ya yi Allah-wadai da abin da ya kira mummuna mulki na inna-naha,, sannan kuma ya lashi takobin yakar wadanda ya ce sun ci amanar al’ummar Mali.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Babban masallacin Djenne da ke Mali na daya daga cikin fitattun ababan tarihi a Afirka

Duk da ya ce ba zai tsaya takarar neman wani mukami ba, amma ana ganin zai iya ci gaba da zama barazana ko kuma mai tasirin sauya al’amura a siyasar kasar ta Mali.

Da farko dai malamin addinin Musuluncin mai goyon bayan shugaban kasar na yanzu ne, Ibrahim Boubacar Keïta, to amma sannu a hankali ya zamo mai sukar shugaban, yana kuma kira da a koma ga abin da ya kira akida ko tsarin dabi’u na Musulunci na ainahi da aka sani.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kogin Isa na Nijar shi ne babbar hanyar sufuri da kasuwanci na Mali

Ibrahim Boubacar Keita ya kama mulki a watan Satumba na 2013, tare da alkawarin hada kan kasar bayan rikice-rikice daban-daban da suka hada da na ‘yan tawaye da juyin mulki da kuma masu tayar da kayar baya na Musulunci, wadanda ke ikirarin Jihadi.

Haka kuma Sheik Mahamoud Dicko a baya ya rika suka ga ‘yancin ‘yan luwadi da madigo da dangoginsu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sojojin Faransa sun shiga kasar bayan da masu ikirarin Jihadi suka kwace wasu sassa na kasar ta Mali

A wata alama da ke nuna cewa an dauke shi ko abin da yake fada da muhimmanci, a ranar Juma’a kotun tsarin mulki ta kasar ta Mali, ta fitar da wata sanarwa, wadda a cikinta take gargadin kafa wata jam’iyyar siyasa bisa akidar kabilanci ko addini.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...