
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmad Umar Fintiri ya ziyarci kasuwar Yola domin jajantawa yan kasuwar da iftila’in gobara ya shafa.
Akalla shaguna 10 ne suka kone kurmus a yayin gobarar.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter gwamna Fintiri ya tabbatarwa da yan kasuwar goyon bayan gwamnatinsa domin su sake gina shagunansu.
Gwamnan ya kuma basu tallafin miliyan 5 kana yayin alkawarin hada gwiwa da sauran hukumomi domin kara tallafa musu.
