FIFA: Da yiyuwar a mayar da gasar cin kofin duniya duk bayan shekara biyu

Akwai masu ra'ayin cewa FIFA na son yin garambawul din ne da nufin samun ƙarin kudin shiga
Akwai masu ra’ayin cewa FIFA na son yin garambawul din ne da nufin samun ƙarin kudin shiga

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA na shirin gudanar da wani zama ta intanet, don yin garambawul a gasussukan ƙwallon ƙafa na maza da na mata.

Daga cikin muhimman abubuwan da za a tattauna akwai batun mayar da buga gasar cin kofin duniya duk bayan shekara biyu a maimakon shekara huɗu.

A cewar sanarwar da FIFA ta fitar ”mafi rinjayen mambobi sun aminta da yin garambawul ga jadawalin wasannin maza da na mata.”

Tuni FIFA ta kafa kwamitin da zai tattauna garambawul ɗin, a ƙarƙashin daraktan kula da ci gaban ƙwallo a duniya wato Arsene Wenger, da kuma takwararsa a bangaren mata Jill Ellis.

Sai dai kuma hukumomin da ke wakilitar nahiyoyi kamar hukumar shirya ƙwallon ƙafa ta Turai wato UEFA da kuma CAF ta Afrika da kuma Conmebol ta kudancin Amurka, sun nuna adawa da buga wasan cin kofin duniya duk bayan shekara biyu.

A cewar mai horar da tawagar ƙwallon ƙafa ta matan Ingila Sarina Weigman ” idan a ka yi haka ba a tausaya wa yan ƙwallo ba.”

Ta ƙara da cewa ”akwai gasussuka masu ƙayatarwa a Turai, ga gasar Olympics sannan kuma uwa uba gasar cin kofin duniya.”

”Idan a ka ce za a riƙa buga waɗannan gasussuka masu muhimmanci kusa da kusa yaushe a ke so ƴan ƙwallo su huta?” Inji Weigman.

A nata ɓangaren ƙungiyar masu horar da ƴan wasa ta Turai AEFCA ta rubuta wa UEFA takardar nuna goyon bayanta kan hawa kujerar naƙi.

Akwai masu ra’ayin cewa FIFA na son yin garambawul ɗin ne da nufin samun ƙarin kudin shiga.

To amma wani bincike da a ka gudanar ya nuna cewa mafi yawan masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya na sha’awar a riƙa buga gasar cin kofin duniya ɓangaren maza duk bayan shekara biyu.

More from this stream

Recomended