Fashewar sinadarai ta yi ta′adi a Jamus | Labarai

Akalla mutum biyu sun rasa rayukansa wasu 31 suka jikkata yayin da wasu ma’aikata biyar kuma suka bata, sakamakon wata fashewar da ta auku a wani kamfanin harhada sinadarai a birnin Leverkusen da ke yammacin Jamus.

Sinadarai masu hadari ga lafiya sama da dubu biyar ne ake hadawa a cibiyar da gobarar ta tashi a cikinta da safiyar Talata. Gobarar ta kuma kama wani defon mai da ke kusa da wajen.

Hukumar da ke kare jama’a daga bala’o’i a Jamus, ta bayyana hadarin a matsayin wata babbar barazana tare da bukatar mazauna kewayen yankin na Leverkusen da su kasance cikin dakuna, sannan a rurrufe kofofi gami da tagogi.

Akwai ma wata cibiyar makamanciyar wannan da ta kusa yin bindiga, sai dai jami’an kwana-kwana sun ce sun shawo kanta.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

Ɗan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...