Europa: Arsenal ta gama shirya bikin cin kofi

Unai Emery

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Abokan hamayya na Landan Chelsea da Arsenal za su fafata a wasan karshe na cin kofin Turai na Europa a Larabar nan a birnin Baku.

Akwai rade-radin cewa wasan na babban birnin kasar Azerbaijan, zai kasance na karshe ga kociyan Chelsea maurizio Sarri, ko sun yi nasara ko kuma an doke su.

Kociyan dan Italiya ya ki ya ce komai a kan rahotannin da ake yadawa da ke nuna cewa zai koma kungiyar Juventus.

A kan hakan ya mayar da martani ne kawai cewa , har yanzu yana da sauran kwantiragi na shekara biyu da Chelsea.

Sarri mai shekara 60 bai taba cin wani babban kofi ba a matsayinsa na kociya.

Amma takwaransa na Arsenal Unai Emery ya dauki kofin na Europa har sau uku a Sevilla tsakanin shekara ta 2014 da 2016.

Haka kuma kungiyar Sarri din, Chelsea ita ma ba ta samu wata nasara ba sosai a Turan.

Yayin da Chelsea ta ci kofin na Europa League a 2013, shekara daya bayan ta dauki kofin Zakarun Turai na Champions, ita kuwa Arsenal rabonta da cin wani kofi tun bayan da ta dauki tsohon kofin da aka daina gasarsa yanzu na European Cup Winners Cup a 1994.

A saboda hakan ne kociyan na Gunners ya ce kawo karshen wannan kamfa ko jira na shekara 25, yake zaman babban burinsa a Azerbaijan,

duk da cewa wasan shi ne dama ta karshe ga kungiyarsa ta samu gurbin shiga gasar zakarun Turai ta kaka mai zuwa, bayan shekara biyu da ta kasa samun zuwa.

Kociyan dan Spaniya ya ce, burinsu biyu ne a wasan, amma babba daga ciki shi ne su dauki kofin.

Buri na biyun kuwa shi ne su samu nasara domin zuwa gasar Zakarun Turai ta gaba.

Emery ba ya ganin cewa abokana karawar tasu, Chelsea ba su dauki wasan da muhimmanci ba, wai ko dan sun riga sun samu gurbin zuwa gasar ta Turai ta gaba bayan da suka gama gasar Premier a matsayi na uku.

Kociyan ya ce kowane kofi yana da muhimmanci a wurinsu haka ita ma Chelsea tana da wannan fata.

Sai dai ba kamar Chelsea ba, Arsenal tuni har ta riga ta shirya yadda za ta yi tattakin bikin murnar cin kofin na Europa a Islington a ranar Alhamis, idan har ta yi nasara.

Amma kuma kyaftin din Chelsea Cesar Azpilicueta ya ce, lalle Arsenal ta yi shirin bikin, amma fatansu shi ne su bata musu wannan shiri, Chelsea ta cinye kofin.

Ya kara da cewa su ba su shirya irin wannan biki ba, amma hakan ba yana nufin ba sa cike da burin daukar kofin ba ne.

Ya ce za su yi duk abin da za su iya yi, domin wannan shi ne wasa na karshe na wannan doguwar kaka.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...