eNaira: Hanya 10 ta soma amfani da tsarin kudin intanet na Najeriya

Shugaban Najeriya

Asalin hoton, @CBN

Babban bankin Najeriya ya bayyana hanyoyin da za a yi amfani da sabon tsarinsa na kuÉ—in intanet da ake kira eNaira.

A ranar Litinin ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙaddamar da kuɗin na intanet.

e-Naira tsarin kuÉ—in Najeriya ne za a yi hada-hada ta intanet. Wannan ne karon farko da Najeriya ta rungumi amfani da kudin na intanet.

Asalin hoton, @CBN

Bayanan hoto,
Yadda Buhari ya kaddamar da eNaira

A cewar CBN eNaira zai zama wata hanya mai inganci ta huldar cinikayya da kudin Naira da kasar ke amfani da ita.

Hakan na nufin a matsayin al’umma za su iya amfani da nairar ta intanet wurin sayen kaya a kasuwa kamar yadda suka saba yi da takardar kudin naira.

Kuma ma’aikatu da hukumomin gwamnati za su iya amfani da tsarin wajen karÉ“ar kuÉ—aden shiga na gwamnati da kuma biyan haraji.

Babban bankin Najeriya ne ke da alhakin kula da tsarin. Kuma CBN ya bayyana hanyoyin soma amfani da sabon tsarin kuÉ—in na intanet, kamar haka:

  • Za a fara sauke manhajar eNaira a kasuwar manhajar Google wato Google Play Store ga masu amfani da wayar Android
  • Za a nemi manhajar eNaira a sauke a waya
  • Bayan an sauke an buÉ—e manhajar za a fara yin rijista inda aka rubuta “Signup”
  • Za a zaÉ“i bankin da mutum yake mu’amula da shi
  • Za a saka lambar waya da kuma bayanan sirri
  • Wurin rijista za a rubuta cikakken suna da ranar haihuwa da asalin jihar mutum da kuma lambar bankin da ake mu’amula da shi da lambobin BVN
  • Idan an kammala rijista za a tura wa mutum saÆ™o a adireshin Imel da ya bayar domin tabbatarwa
  • Za a amince da tsarin eNaira idan an danna “Activate Wallet”
  • Domin fara aiki da eNaira za a saka suna da lambobin sirri wanda aka yi rijista
  • Idan ya buÉ—e mutum zai ga asusunsa na eNaira

Yadda za a saka da cire kuÉ—i a asusun eNaira

Wanda ya buÉ—e asusun eNaira zai iya saka kuÉ—i a ciki nan take daga asusunsa na banki.

Kamar yadda mutum zai buÉ—e asusun eNaira haka ma bankuna suna da tsari da CBN ya yi tanadi domin su.

Za a iya samun eNaira a manhajar bankin da mutum yake mu’amula da shi – akwai tsarin saka kuÉ—i da cire wa da za a zaba daga manhajar banki domin turawa da cire kuÉ—i daga asusun eNaira.

Mutum zai saka adireshinsa na Imel da aka yi masa rijista da lambobinsa na BVN – sai a saka lambobin sirri na asusun eNaira.

Za a turo wa mutum wasu lambobi a wayarsa da zai yi amfani da su domin tabbatar da cire wa ko saka kuÉ—i.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...