
Hukumar EFCC dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta ce jami’anta sun kama wasu yan kasar China 13 kan zargin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar Kwara.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin ta na Twitter a ranar Alhamis ta ce mutanen da aka kama a unguwar GRA dake Ilorin sun hada da maza 12 da kuma mace daya.
Kamen da ofishin shiyar hukumar na Ilorin ya yi an yi shi ne biyo bayan gamsassun bayanai sirri akan ayyukansu da suka haɗa da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma kin biyan kudin haraji ga gwamnatin tarayya kamar yadda doka ta tanada.
Mutanen da aka kama sun haɗa da Guo Ya Wang ( shekaru 36), Lizli Hui (shekaru 42), Guo Jian Rong (shekaru 36), Lizh Shen Xianian (shekaru 37), Lishow Wu (shekaru 26), Guo Pan (shekaru 38), Lia Meiyu (shekaru 53), Guo Kai Quan (shekaru 36) Lin Pan (shekaru 50).
Sauran su ne Ma Jan (shekaru 38), Wendy Wei Suqin (shekaru 31), Li Zhinguo Wei (shekaru 29), and Xie Zhinguo (shekaru 53).
“Bayan da aka yi musu tambayo yi sun amsa cewa su ma’aikatan kamfanin China ne da aka fi sani da W. Mining Global Service Limited dake Olayinka a karamar hukumar Ifelodun ta jihar.” a cewar sanarwar.
Har ila yau binciken ya bayyana cewa wasu daga cikin su basu da shedar yin aiki a Najeriya sun shigo kasar ne da biza ta ziyara.