EFCC Ta Kama Tsohon Ministan Buhari Da Zargin Laifin Satar Naira Biliyan 22

Hukumar EFCC dake yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta tsare tsohon ministan wutar lantarki, Sale Mamman kan zargin sa da karkatar da kuɗin da yawansu ya kai biliyan 22.

Mamman ya rike muƙamin ministan wutar lantarki daga shekarar 2019 zuwa 2021 lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya sauke shi daga kan muƙamin sa.

An tsare shi ne bayan da ya amsa gayyatar da EFCC ta yi masa zuwa ofishin ta dake Abuja.

Wasu majiyoyi a hukumar EFCC sun bayyana cewa Mamman ya haɗa baki tare da wasu ma’aikatan ma’aikatar wutar lantarki inda suka karkatar da naira biliyan 22 suka kuma raba su a tsakaninsu.

More from this stream

Recomended