EFCC na zargin tsohuwar ministar mata a mulkin Buhari da karkatar da naira biliyan 2

Hukumar EFCC dake yaĆ™i da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta titsiye tsohuwar ministar harkokin mata Pauline Tallen kan zargin azurta kai ta hanyar al-mundahana.

Jaridar The Cable ta gano cewa, Tallen ta isa ofishin EFCC dake Abuja a ranar Juma’a domin amsa tambayoyi kan al-mundahanar kuÉ—in da ya kai naira biliyan biyu.

Duk da cewa kawo yanzu babu cikakkun bayanai kan zarge-zargen da ake mata wata majiya dake hukumar ta EFCC ta ce ana zargin tsohuwar ministar da karkatar da kudaden da suka shafi taron kungiyar matan shugabannin kasashen Afirka kan zaman lafiya da ake kira African First Lady Peace Mission Project (AFLPM) a turance.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...