Ƙungiyar NARTO ta masu motocin sufuri a Najeriya ta dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a faɗin Najeriya baki ɗaya.
An dakatar da yajin aikin ne biyo bayan wani taron ganawa da aka gudanar a tsakanin ƴan ƙungiyar da kuma gwamnatin tarayya a ranar a Abuja bayan da motoci Masu dakon man fetur suka sanar da shiga da yajin aikin.
Shugaban ƙungiyar ta NARTO Yusuf Lawal shi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da aka fitar.
Tun bayan sanar da shiga yajin aikin aka fara samun dogayen layukan man a biranen Abuja da Lagos.