Dan Sudan ya gano sirrin Fir’auna | BBC Hausa

Dala-dala

Hakkin mallakar hoto
Nuri Archaeological Expedition/PearcePaulCreasma

Image caption

Sudan tana da yawan dala fiye da Masar

Wani mai binciken kayan tarihi na karkashin kasa ya yi wa BBC bayani kan irin namijin kokarin da ya yi domin gano kabarin wani Fir’auna a can karkashin wata dala a cikin ruwa.

Pearce Paul Creasman da tawagarsa, su ne mutane na farko da suka shiga cikin hubbaren a shekara 100, kuma a wannan lokaci yana da matukar wuya a iya shiga wurin saboda zurfin ruwan da ke wurin.

Mista Creasman ya bayyana wa shirin labarai na BBC Newsday cewa wannan ne karon farko da aka gudanar da wani aikin binciken kayan tarihi na karkashin kasa a can cikin ruwa a Sudan, a wurin binne sarakunan zamanin da na Nuri.

Ya gano wasu ‘yan mutum-mutumi da aka yi da yunbu da kuma zinariya.

Hakkin mallakar hoto
Nuri Archaeological Expedition/ PearcePaulCreasman

Hakkin mallakar hoto
Nuri Archaeological Expedition/PearcePaulCreasman

“Zinariyar sadaka da aka ajiye a wurin har yanzu tana nan, wadda ta hada da wadannan ‘yan kananan surorin masu kama da na gilashi wadanda aka lillebe su da zinare. Duk da cewa ruwa ya bannata gilashin da ke kasan wurin to amma har yanzu ana iya ganin sauran zinaren a wurin” kamar yadda ya sheda wa BBC

Mai binciken ya yi amanna wadannan kayan tarkacen na sadaka na wani karamin Fir’auna ne da ake kira Nastasen, wanda ya mulki Daular Kush daga shekarar 335 zuwa 315 (kafin bayyanar Annabi Isa a.s).

Idan da ba domin zurfin ruwan wurin ba, wanda ya sa mutane da ya wa ba za su iya zuwa wurin kabarin ba, to da tuni barayi sun sace wadannan kayan zinare.

Mr Creasman ya gaya wa BBC cewa sai da tawagar, ” ta yi gina iya iyawarta, har can kasa da matakala 65, wanda ta haka suka kai ga kofar hubbaren. Ya ce sai da suka kai kamar zurfin mataka 40 a kasa, sannan suka kai ga ruwa, wanda dahga nan ne kuma suka san cewa, to fa daga nan kuma sauran ramin da za su yi za su kasance a cikin ruwa ne da zai shafe su har kai”.

Hakkin mallakar hoto
Nuri Archaeological Expediton/PearcePaulCreasman

Image caption

Ramin da aka yi har aka iya shiga hubbaren

Ya ce da suka ga aikin da ke gabansu, da farko sun yi tunanin amfani da irin manyan goran nan na karfe mai dauke da iskar da ake shaka irin wanda ‘yan kurmau suke amfani da shi, idan za su shiga karkashin ruwa, to amma sai suka ga ba zai yi dadin shiga ba, a maimakonsa sai suka yanke shawarar amfani da wata mesa da za ta rika turu musu iskar shakar daga waje, a watan Janairu.

Ya bayyana abubuwan da suka gano da cewa suna da muhimmanci sosai:

“Akwai sassa uku, wadanda aka yi musu ado mai kyau a cikinsu daga sama, wadanda sun kai kamar girman ‘yar karamar motar bas, za ka shiga cikinsu ne daga wannan ka wuce ka je na gaba, tun daga nan za ka fahimci cewa kana cikin wani hubbare ne, kuma daga nan za ka fara fahimtar irin kayan sirrin da ke cikin wurin.” In ji shi

Wurin na daga wani bangare na hubbaren zamanin da na Nuri wanda ya kai fadin eka 170 a yankin arewacin Sudan.

To wadannan dala-dalai na nuna cewa makabarta ce ta ‘yan sarautar Kush, wadanda a wani lokaci ake bayyana su a matsayin ”bakaken Fir’aunoni”.

Ita wannan daula ta Kush ta yi zamani na daruruwan shekaru, kuma a karni na takwas (kafin zuwan Annabi Isa a.s), ta kama Masar, inda ta mulke ta tsawon kusan karni daya.

Wani bambanci daya tsakanin dala-dalar da ke Sudan da kuma wadanda aka fi sani na Masar shi ne, su na Sudan a kasansu ake binne sarakuna mai makon a cikinsu.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...