
Mamba a majalisar wakilai ta tarayya kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Edo da ya sauka, Marcus Onobun yayi hatsarin mota a ranar Laraba.
Hatsarin ya faru a wajejen Ekpoma-Auchi a babbar hanyar Benin zuwa Abuja a lokacin da dan majalisar ke hanyarsa ta komawa Abuja.
Tun da farko Onobun ya yin shirin hawa jirgi ne zuwa Abuja amma sai ya makara bai samu ba hakan yasa ya yanke shawarar tafiya a mota.
Dan majalisar dake wakiltar kananan hukumomin Esan West, Esan Central da kuma Igueben ya samu rauni a hatsarin.
Shugaban jam’iyar PDP na jihar Edo, Tony Aziegbemi ya tabbatar da faruwar hatsarin.
Ya ce Onubun na cigaba da samun kulawar likitoci a asibitin koyara na Jami’ar Benin.