Dalilin da ya sa Liz Truss ta ajiye muƙaminta na firaministar Birtaniya—BBC Hausa

Asalin hoton, Getty Images

Liz Truss ta yi murabus daga muƙaminta na Firaministan Birtaniya bayan mako shida kacal. Ga Abubuwan da ya kamata ku sani game da ita.

Ita ce firamininsta mafi ƙarancin daɗewa kan mulkin Birtaniya

Liz Truss ta maye gurbin Boris Johnson a matsayin jagoran jam’iyyar Conservative kuma ta zama firaminista a ranar 6 ga watan Satumba, sannan ta yi murabus bayan kwana 45 kacal.

Shugaban da ya shafe lokaci mafi ƙaranci a kan mulkin kafin yanzu shi ne George Canning wanda ya yi kwana 119 a ofis a shekarar 1827.

Ta afka cikin matsaloli cikin sauri

Bisa goyon bayanta, ministan harkokin kuɗi Kwasi Kwateng ya sanar da rage biyan kuɗin haraji na biliyan 45 a mako na uku da fara mulkinta cikin abin da suka kira “ƙaramin kasafi”.

Sai dai an zargiNshirin da haddasa matsalolin tattalin arziki masu girma.

Duk da yadda Truss ta dage cewa shi ne “abin da ya kamata”, yanzu an soke dukkan shirin – kuma aka sauke Kwateng daga muƙaminsa.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar jam’iyyarta sun fara sukarta

Gwamman ‘yan majalisa daga jam’iyyarta sun fara kira da ta sauka, inda daga baya Sakatariyar Harkokin Cikin Gida Suella Braverman ta sauka.

Dolenta ta nemi tsoffin abokan hamayyarta, Grant Shapps da Jeremy Hunt don su cike gurbin da aka bari.

Ta ce ba za ta iya cika alƙawarin da ta ɗauka ba

Cikin jawabinta a Fadar Downing Street, ta ce: “Na lura cewa ba zan iya cika alƙawarin da na ɗauka ba wanda a kansa ne ‘yan Jam’iyyar Conservative suka zaɓe ni.”

Ta doke tsohon minista Rishi Sunak kafin ta zama firaminista

Iya ‘yan jam’iyyarta ne kaɗai suke da ikon zaɓarta a matsayin shugaba.

Sunak ne kan gaba a ƙuri’un da ‘yan majalisar suka kaɗa amma da aka zo zagayen ƙarshe sai mutum fiye da 80,000 suka zaɓe ta a kan Sunak, kuma ta yi nasara.

Ba mu san wanda zai maye gurbinta ba

Cikin mako mai zuwa za a fara fafatawa wajen neman mulkin. Za ta ci gaba da mulkin har sai an samu wanda zai maye gurbin nata.

Ita ce firaminista ta ƙarshe da Sarauniya Elizabeth II ta naɗa

Sarauniya ta naɗa Liz Truss ‘yan kwanaki kafin rasuwarta, kuma ta fara shugabanci da makokin kwana 10.

Ta yi aiki a matsayin masaniyar tattalin arziki

Bayan ta kammala jami’a, ta yi aiki tare da kamfanonin Shell da kuma Cable & Wireless, sannan ta auri masanin harkar kuɗi Hugh O’Leary a shekarar 2000.

Suna da ‘ya’ya mata biyu. Suna zaune a Thetford da ke yankin Norfolk na Ingila.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...