‘Dalilin da ya sa aka kori shugabar ma’aikata’

A daren Laraba ne dai wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana nadin sabuwar shugabar ma’aikatan tarayyar kasar Dr Mrs Folashade Yemi-Esan.

Wanda hakan kai-tsaye ke alamta cewa an kori tsohuwar shugabar ma’aikatan wadda rikici ya dabaibaye, Mrs Wilfred Oyo-Ita.

Sanarwar ta ce ‘An cire Oyo-Ita ne daga mukaminta domin a bayar da damar kammala binciken da hukumar bincike ta EFCC ke yi a kanta’.

Bayanin da ke cikin sanarwar ya nuna cewa an bukaci Oyo-Ita da ta fara wani hutun da ba ce ga ranar dawowarta ba.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawar Najeriya ta EFCC dai na binciken tsohuwar shugabar ma’akatan gwamnatin tarayya ce bisa zargin ta da hannu a badakalar wata kwantaragi ta kudi biliyan 3.

A baya dai hukumar ta EFCC ta kira tsohuwar shugabar, inda ta yi mata tambayoyi a kan al’amarin da ya jibanci kwantaragin.

Sabuwar shugabar ma’aikatan da aka nada Mrs Folashade Yemi-Esan kafin nadin nata ita ce babbar sakatariya a ma’aikatar man fetur ta Najeriya.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...