Da gaske ne mata sun fi maza yawa a duniya?

Wasu mata suna daukar hoton selfie
Hakkin mallakar hoto
Google

—BBC Hausa

Image caption

Masana sun ce zuwa shekarar 2040 yawan al’ummar Najeriya zai ninka sau uku

Babu mamaki idan ka ji tambaya cewa “tsakanin maza da mata wadanne ne suka fi yawa?” Wucewa za ka yi abinka, ba ma sai ka bayar da amsa ba bisa tunanin cewa mata sun fi yawa.

Kila saboda matan da suka taru a biki na karshe da aka yi a gidanku ko a makota suna da yawan da sun wuce kirge, ko kuma kila matan gidanku sun fi maza yawa.

Kai saurayi kana da ‘yan mata hudu ko biyar, ke kuma budurwa kila samarinki sun fi goma, saboda haka kowa na gina tunaninsa kan tsammani.

Ko ma dai mene ne, wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ne ya bayayana cewa yawan al’ummar duniya ya kai biliyan 7,713,468,000, inda ya bayyana cewa maza sun dara mata yawa.

Rahoton ya bayyana cewa Najeriya na da yawan mutane miliyan 200,964,000, inda maza suka kai miliyan 101,832,000 mata kuma miliyan 99,132,000.

Hakan yana alamta cewa maza sun dara mata yawa da milyan 2,700,000 a Najeriya.

Su kuwa masana cewa suke nan da shekarar 2040 yawan al’ummar kasar zai ninka har sau uku, kuma ba tare da wasu kayayyakin more rayuwa ba.

  • ‘Yan Najeriya sun fi talauci a mulkin Buhari – The Economist
  • Shin talauci na karuwa a Najeriya?

Ganin cewa wannan rahoto ya ci karo da imanin mafi yawan mutane na cewa mata sun fi maza yawa, mun ji ta bakin ma’abota shafukanmu na sada zumunta.

Mun tambayi masu bibiyarmu a shafukan sada zumunta: “Tsakanin maza da mata wadanne ne suka fi yawa a Najeriya a ganinku?”, kuma mun samu amsoshi iri daban-daban.

Su ma masu bibiyarmu a Facebook sun bayyana mabambantan ra’ayoyi kan wadanda suka fi yawa tsakanin maza da mata.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...