Da gaske ne Buhari ya kori ma’aikatan Osinbajo?

Buhari Osinbajo

A farkon makonnan ne dai jaridu da kafafen sada zumunta suka dauki dumi inda wani labari ya yi ta karakaina cewa Shugaba Buhari ya kori ma’aikata masu taimaka wa mataimakinsa, farfesa Yemi Osinbajo.

Jaridu a kasar sun ta buga labarin cewa shugaba Buhari ya sallami 35 daga cikin ma’aikatan mataimakin nasa.

An dai ce farfesa Osinbajo na da mataimakan da suka fi na shugaba Buhari yawa, inda rahotanni suka ce an nada wasunsu ne lokacin da Osinbajo yake rikon kwarya a lokacin da shugaba Buhari ya kwashe fiye da kwana 130 yana jinya a London a 2017.

Rahotannin sun rawaito wasu majiyoyin cikin fadar shugaban kasa na cewa korar ma’aikatan 35 ya zama dole kasancewar an dauke wasu ayyuka daga karkashin ofishin Osinbajo zuwa wasu ma’aikatu.

Idan dai ba a manta ba, a zangon farko da mulkin shugaba Buhari, ofishin mataimakin shugaban ne ke kula da tafiyar da tattalin arzikin kasar da kuma shirye-shiryen tallafa wa ‘yan kasa na Social Investment Programmes.

Sai dai a ranar Juma’ar nan ne mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya tabbatar da abin da ya kira ‘rage’ yawan ma’aikata a shafinsa na Twitter:

Malam Garba Shehu yana cewa “Fadar shugaban kasa na son tabbatar da aikin yi wa tsarin mukaman gwamnati kwaskwarimar da ba a taba gani ba a baya ba, da ya shafi mukaman siyasa da dama da ko dai aka soke su ko kuma ba a sabunta su ba a zango na biyu na mulki.”

Garba Shehu ya ci gaba da cewa shugaban kasa ne ya bayar da umarnin yin hakan a wani mataki na rage kashe kudaden gwamnati kasancewar mukamai sun yi yawa a fadar shugaban kasa al’amarin da ke janyo kashe kudade fiye da kima.

To sai dai Malam Garba Shehu ya nuna cewa ofishin mataimakin shugaban ne da kansa ya dauki matakin rage ma’aikatan nasa domin bin ka’idar da shugaban ya shimfida:

‘Rage wa Osinbajo karfin iko’

Batun da yake ta kai komo a kafafen watsa labaran Najeirya a baya-bayan nan shi ne cewa wasu ‘tsiraru’ masu fada a ji a fadar shugaban kasa na ta kokarin rage wa mataimakin shugaban, farfesa Yemi Osinbajo karfin iko.

Ana ta hasashen cewa tun bayan da gwamnatin shugaba Buhari ta yi kome zango na biyu ake ta kwashe wasu ayyuka daga ofishin Osinbajo.

Misali a karon farko, aikin tafiyar da tattalina arzikin kasa da shirye-shiryen tallafa wa ‘yan kasa na Social Investment Programs da hukumar NEMA mai kai dauki gaggawa na karkashin ofishinsa.

Amma yanzu duk an dauke su daga karshin ofishin mataimakin shugaban inda aka mayar da su karshin ma’aikatar agaji da jin kai da Sadiya Umar ke jagoranta.

Har wa yau, batun kin bai wa farfesa Osinbajo rikon kwarya bayan tafiyar shugaba Buharin kasashen Saudiyya da Burtaniya, ya kara jefa ‘yan kasar cikin zulumin karfin iko na mataimakin shugaban.

A farkon makon nan ne dai shugaban ma’aikatan kasar, Abba Kyari ya yi tafiyayya har Landan don kai wa Shugaba Muhammadu Buhariya dokar hakar mai domin ya sanya mata hannu.

Watakila faruwar irin wadannan nan abubuwan ne ya sa kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta fito ta bara ranar Talata.

Afenifere ta ce ana mayar da mataimakin shugaban Æ™asar Farfesa Yemi Osinbajo É—an kallo a tafiyar da al’amuran Najeriya.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...