Cututtukan da ya kamata a bi su a hankali a lokacin azumi

Cuta

Asalin hoton, Getty Images

Al’umar musulmi a faÉ—in duniya na ci gaba da azumtar watan Ramadan domin ibada ga mahaliccinsu.

Azumi na nufin daina cin abinci ko kusantar iyali daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana da nufin neman yardar Ubangiji.

To sai dai kamar yadda likitoci suka yi bayani akwai nau’in wasu cututtuka da ke tasowa ko su Æ™ara munana a lokacin azumi sakamakon daina cin abinci a tsawon wuni.

Haka kuma a gefe guda likitocin sun ce akwai nau’in wasu cutuka kuma da ake samun sauÆ™i musamman a lokacin azumin.

Cututtukan da ke tashi lokacin azumi

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Mu’awiya Aliyu ma’aikaci a hukumar lafiya ta jihar Katsina ya ce a lokacin azumi akwai cutuka kamar:

Ulcer/Gyambon ciki: Cuta ce da ke sanya cikin mutum ya yi ta jin zafi kamar an barbado borkono a cikin mutum.

”Hakan na faruwa ne sakamakon Æ™arancin abinci a cikin É—an adam,, kuma mai É—auke da cutar zai riÆ™a jin tana tashi a lokacin da bai ci abinci ba”, in ji Daktra Mu’awiya.

Cutar Koda: Dakta Mu’awiya ya ce akwai wasu nau’ikan cutakan da suke shafar koda, waÉ—anda rashin shan ruwa ke haddasa su.

Likitan ya ce masu dauke da irin wannan cutar, a kan ba su shawara da su riƙa yawan shan ruwa akai-akai.

Cutar mafitsara: Ita ma wannan cuta ce da ke bukatar yawaita shan ruwa kasancewa ruwan kan taimaka wajen wanke ciwon da ke damun mafitsarar.

Wasu nau’in cutuka da ke haddasa samun duwatsu a cikin kodar mutum ko mafitsara, su ma waÉ—annan cutuka a kan buÆ™aci mai É—auke da su da ya riÆ™a yawan shan ruwa wanda zai taimaka wajen narkar da duwatsun.

Likitan ya ce ”irin waÉ—an nan cutuka su ma suna yawan tashi musamman a lokacin azumi”.

Haka kuma likitan ya ce akwai cutar Matsarmama wadda ita ma ke buƙatar yawan shan ruwa.

Cutakan da ake samun sauƙinsu a lokacin azumi

Haka kuma Likitan ya zayyana wasu nau’ikan cutuka da ya ce ake samun saukin tashinsu musamman a lokacin azumi.

Cutukan Zuciya: Likitan ya ce dama mafi yawan abin da ke haddasa cutukan zuciya shi ne yawaitar kitse a jikin zuciyar.

Cukar kansa: Wasu dalilan cutar su ne girma na wuce kima da wani É“angare na jikin mutum ke yi, ”to a wannan yanayin da mai cutar ke azumi to ka ga babu abincin ma da mutum zai ci balle cutar ta habaka”, in ji likitan.

Cutar Amai da gudawa: Likitan ya ce ”dama ta hanyar cin wani nau’in abinci da ya gurÉ“ata ko ya cuÉ—anya da Æ™wayar cutar ne ke haddasa shi, to amma idan ana azumi, ba a ma ci abincin ba balle ya ci Æ™wayar cutar ba”.

Cutar hanta: Hanta ita ce ke tace duka wani abinci domin fitar da abu mai amfani da marar amfani daga cikin abincin da mutum ya ci, kamar yadda likitan ya bayyana.

Ya ce ”idan mutum na azumi hantar za ta samu sauÆ™in aiki, to a nan hantar kan samu sauÆ™i sosai a lokacin da babu abincin da hantar za ta tace”.

Cutar ƙiba: Likitan ya ce ƙiba ma cuta ce wato a cewarsa kitse ne ke taruwa a cikin tumbin mutum, ko ƙirjinsa ta yadda zai rufe zuciya ko ƙodar mutum.

Likitan ya ce azumi kan taimaka wajen rage ƙibar kasancewar lokacin cin abincin mutum ya zama ƙayyadajje.

Abincin da ya kamata a riƙa ci da azumi

Asalin hoton, Getty Images

Likitan ya ce akwai wasu na’ikan abinci da ya kamata mutane su riƙa ci ko sha musamman lokutan shan ruwa ko sahur, waɗanda a cewarsa za su taimaka wajen kwantar da cutukan da ke tashi musamman a lokutan azumi.

Dakta Mu’awiya ya ce irin nau’ikan abincin kan taimaka wajen kwantar da cutukan kasancewar idan aka yi sahur da su to mutum zai daɗe bai ji yunwa ba idan gari ya waye.

Likitan ya ce duk wani abinci nau’in Protien kan taimaka wajen daɗewa a jikin mutum, kasancewar abincin ba ya narkewa da wuri.

Sannan likitan ya shawarci mutane da su guji yin amfani da ruwa ko lemukan sanyi musamman a lokacin shan ruwa.

Dakta Mu’awiya ya ce ba laifi mutum ya fara da ruwa amma ba mai sanyi sosai ba.

‘’Amma idan mutum zai iya ya daure ya fara da ruwa mai dumi, wanda zai taimaka wajen narkar da kitsen da ke cikin mutum, amma idan ya fara da ruwan sanyi to ƙara daskarar da kitsen zai yi’’, in ji Dakta Mu’awiya.

Likitan ya ce lemukan sanyi ba sa taimaka wa jiki ko lafiyar mutum, hasalima a wasu lokutan ya ce cutar da jikin mutum suke yi kasancewar suna É—auke da sinadarin sikari a cikinsu.

Ya kuma shawarci masu azumin da su riƙa amfani da abinci mai ɗauke da sinadarin Glucose a cikinsu, kasancewa su ne za su taimaki mutum wajen maido masa da ƙarfinsa da ya rasa a lokacin da yake azumi.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...