COVID-19: Abinci biyar da ke kare garkuwar jiki

Mangoro yana inta garkuwar jiki

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Masana ilimin abinci sun bayyana cewa akwai bukatar mutane su rika shan cin nau’in abinci da ‘ya’yan itace domin inganta garkuwar jikinsu.

Masanan sun ce cin wadannan na’ukua na abinci zai yi tasiri sosai a jikin mutum ta yadda zai ba shi kariya daga cututtuka irin su cutar korona.

Hajiya Zainab Ujudud Shariff, wata masaniyar abinci da tsarin amfani da shi ta shaida wa BBC nau’ukan abincin da suka kamata a rika ci domin inganta garkuwar jiki:

Zogale

Cin zogale da koren tattasai da kuli-kuli ko kuma tafasa shi a yi sirace da shi sannan a sha ruwansa. Kazalika za a iya mayar da shi gari sannan a rika sanya shi a cikin shayi ana sha. Binciken kimiyya ya gano cewa zogaye yana gyara garkuwar jiki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Zobo

Shan zobon ruwan da aka hada da citta da kanimfari ba tare da suga da yawa ba yana gyara garkuwar jiki.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

‘Ya’yan itace biyar da ke kare garkuwar jiki

Mangoro

Mangoro yana dauke da sinasarin phytonutrients da phytochemicals da kuma anti-oxidantant property. Suna karfafa garkuwar jiki. Don aka yana da matukar amfani a wanke mangoro kafin a sha. Yana da kyau a hada mangoro da goba da kankana wuri guda ta hnayar yanka su sanna a sha su lokaci guda.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kindiro

Kindirmo musamman wanda aka tatso daga jikin saniya kai tsaye yana ingata garkuwar jiki. Amma babu laifi idan mutum ya yi amfani da kindirmo dan kanti.

Citta da kanimfari

Citta da kaninfari suna gyara garkuwar jikin mutum. A sanya su a cikin ruwan zafi a sha su.

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ĆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...