Coronavirus: Gwamnatin Najeriya ta yafe wa gidajen rediyo kashi 60 na bashin da ake binsu

Lai Mohammed
Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta sanar da yi wa gidajen rediyo da talbijin rangwamin kashi 60 cikin 100 na basukan da ta ke binsu.

Gwamnatin dai tana bin wasu kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin bashin kudade da ya kai naira biliyan bakwai da miliyan dari takwas.

Cikin wata sanarwa, ministan yada labaran kasar Lai Muhammad ya ce gwamnati ta dauki matakin ne don rage musu radadin rashin kudaden shiga saboda annobar cutar korona.

A cewar Lai Muhammad duk wadanda ake bi bashin su hanzarta biyan kashi arba’in cikin dari na abin da ake binsu cikin watanni uku.

Sanarwar ta kara da cewa gidajen rediyo da dama a Najeriya ana binsu bashi mai yawa lamarin da yasa wasu ma ke fuskantar barazanar kin sabunta musu lasisin su.

Hajiya Sa’a Ibrahim, Shugabar Kungiyar kafafen watsa labarai na rediyo da talbijin a Najeriya kuma shugabar gidan talbijin na Abubakar Rimi a Kano ta ce sun yi farin ciki da wannan matakin.

“Ko ya ya idan aka yi maka abu, dole za ka yaba za ka ji dadi, abin da yake akwai shi ne an yi abin da za a ce ai da babu gwara ba dadi,”

“Wannan ma tun da ya wuce rabi za a ce an yi hobbasa toh amma dai abin da yake akwai shi ne dole za a bibiya kowa ya ma san matsayin bashin da yake kansa, kafin mu tafi biya din,” in ji Hajiya Sa’a

Tun da farko dai kungiyar ce ta nemi gwamnatin Najeriya ta sassauta mata basussukan da ta ke binsu ne, saboda annobar korona ta durkusar da harkokin tallace-tallace a gidan rediyo da talbijin.

Sai dai Hajiya Sa’a ta kara da cewa “a har kullum idan mutum ya yi maka abin kirki, kafin ka ce za ka iya ko ba za ka iya ba, sai ma ka je ka tantance matsayinka tukuna,”

“Tun da ba abu ne da ya shafi mutum daya ko biyu ba, abu ne da ya shafi kafafen yada labarai masu zaman kansu saboda haka yanzu ne labari ya fito, yanzu kowa yake so ya koma ya duba ya ga,”

“Shin kashi 60 din nan da aka ware, me ne ma nauyin bashin da yake kansa? abin mai yiwuwa ne ko kuwa zamu sake dawowa da kokon bara mu ga yadda za a yi amma dai za mu rubuta sunanmu mu ga yanayin wannan al’amari sannan mu ga mataki na gaba da za mu dauka.” a cewarta.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar dai ta ce duk gidan radiyo ko talabijin din da bai biya bashin da ake binsa ba a cikin watanni uku, wannan sassaucin na kashi 60 cikin 100 da aka cire ya wuce shi.

Ko a kwanakin baya ma sai da gwamnatin Najeriyar ta daukewa wasu kafafen watsa labarai biyan kudaden lasisi na watanni biyu don rage musu radadin da cutar korona ta haifar.

Haka kuma ministan ya ce suna tattaunawa da Kungiyar masu gidajen jaridu ta Najeriya domin ganin irin sassaucin da za a yi musu.

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ĆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...