Copa del Rey: Real Madrid za ta kara fafatawa da Alcoyano

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid za ta kara fuskantar Alcoyano a karawar kungiyoyi 32 a Copa del Rey, bayan da aka raba jadawali.

Karo biye kenan a jere da aka hada kungiyoyin don karawa a kofin da Real za ta fara ziyartar Estadio El Collao don buga wasan farko.

A janairun shekarar nan Real Madrid karkashin Zinedine Zidane ta yi nasara da ci 2-1 a karin lokaci dun da an cire mata dan wasa daya a karawar.

Alcoyano mai buga gasa ta uku a Sifaniya ta kawo wannan matakin kungiyoyi 32 da za su ci gaba da gasar, bayan da ta yi nasara a kan Levante a bugun fenariti.

Barcelona mai rike da Copa del Rey itama za ta fuskanci kungiya ta uku a gasar Sifaniya da za ta ziyarci Linares Deportivo, yayin da Atletico Madrid za ta buga wasan hamayya da Rayo Majadahonda.

Sevilla, wadda take ta shida a kan teburin bana za ta ziyarci mai rike da Copa del Rey shida, Real Zaragoza, wadda ke buga karamar gasa ta biyu wato Segunda, bayan da ta fado daga La Liga a 2012-13.

Za a fara wasannin farko a tsakiyar mako tsakanin 4 zuwa 6 ga watan Janairun 2022.

Jadawalin Copa del Rey da aka yi ranar Juma’a:

  • Atletico Mancha da Real Athletic CLub
  • Rayo Majadahon da da Atletico Madrid
  • Alcoyano da Real Madrid
  • Linares da Barcelona
  • Atletico Baleares da Celta Vigo
  • Real Valladolid da Real Betis
  • Almeria da Elche
  • Mirandes da Rayo Vallecano
  • Cartagena da Valencia
  • Sporting Gijon da Villarreal
  • Eibar da Real Mallorca
  • Fuenlabrada da Cadiz
  • Leganes da Real Sociedad
  • Girona da Osasuna
  • Zaragoza da Sevilla
  • Ponferradina da Espanyol

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...