Chelsea za ta karbo Coutinho; Barca za ta karbo Griezmann | BBC Hausa

Antoine Griezmann

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Chelsea na son karbo dan wasan Barcelona Philippe Coutinho, idan har an dage wa kulub din haramcin sayen ‘yan wasa. (Gianluca di Marzio).

Juventus na shirin kammala yarjejeniya Maurizio Sarri kocin Chelsea. (Independent)

Barcelona tana son sayen dan wasna Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 28 daga Atletico Madrid, sannan tana son ta karbo dan wasan Brazil Neymar da ta sayarwa Paris St-Germain. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Rahotanni kuma sun ce kaftin din Barcelona Lionel Messi ya ce yana son a bude masa shafi na musamman domin tattaunawa da Neymar da abokin wasansa Suarez. (Marca)

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Newcastle United ta tattauna da tsohon kocin AC Milan Gennaro Gattuso domin maye gurbin Rafael Benitez. (Newcastle Chronicle)

Paris St-Germain ta nuna sha’awar karbo dan wasan Belgium da Manchester United Romelu Lukaku, mai shekara 26. (Express)

Bayern Munich ta saka Jerome Boateng a kasuwa kan fam miliyan 20, inda Arsenal da Manchester United ke sha’war dan wasan mai shekara 30, (Bild – in German)

Arsenal za ta saye dan wasan Paris St-Germain mai shekara 27 Thomas Meunier. (Paris United)

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...