
Asalin hoton, Getty Images
Paris St Germain za ta fafata da Real Madrid a wasan zagaye na biyu a Champions League, bayan da aka raba jadawali ranar Litinin.
Za su fara buga wasan farko a tsakaninsu a birnin Paris ranar 15 ga watan Fabrairu, sannan karawa ta biyu a yi a Santiago Bernabeu ranar 9 ga watan Maris.
An kara tsakanin PSG da Real Madrid sau shida, inda Real ta yi nasara a wasa uku da canjaras biyu, inda kungiyar Faransa ta yi nasara daya.
Fafatawar da aka yi tsakanin PSG da Real Madrid:
Champions League ranar Talata 26 ga watan Nuwambar 2019
Champions League ranar Laraba 18 ga watan Satumbar 2019
Champions League ranar Talata 6 ga watan Maris 2018
Champions League ranar Laraba 14 ga watan Fabrairun 2018
Champions League ranar Talata 3 ga watan Nuwambar 2015
Champions League ranar Laraba 21 ga watan Oktobar 2015
Yadda aka raba jadawalin Champions League: