Burtaniya da Amurka sun ce Iran za ta yaba wa aya zaki kan harin jirgin ruwan Isra’ila

A harin da aka kai kan jirgin mai suna Mercer Street a gabar tekun Oman, ya hallaka mutum biyu a ciki

Burtaniya da Amurka sun yi amanna da cewa Iran ce ta kai harin nan na ranar Alhmais kan wani jirgin ruwan dakon mai, da kamfanin wani attajirin Isra’ila ke tafiyarwa, a gabar tekun Oman wanda a lokacin mutum biyu – dan Birtaniya da da dan Romaniya suka hallaka.

Kasashen biyu sun lashi takobin mayar da martani, kan abin da suka ce saba dokokin duniya, yayin da ita kuma Iran ta nanata cewa zargin ba shi da tushe.

Tun bayan wannan hari da aka ce an yi amfani da dan karamin jirgin sama maras matuki wajen kai shi a ranar Alhamis din a kan jirgin ruwan dakon man mai suna MV Mercer Street, mallakar Japan, amma da tuta ko rijistar kasar Liberia, wanda kuma kamfanin hamshakin attajiri, dan Isra’ila da ke da cibiya a London yake tafiyarwa, ake ta tayar da hakarkari a kansa, inda Isra’ila tun lokacin ba ta bata lokaci ba ta zargi Iran.

Sai kuma a yanzu suma, manyan kasashe biyu Birtaniya da Amurka suka bi sahun Isra’ilar kan wannan zargi, tare da alkawarin cewa Iran, wadda ta ce zargi ne maras makama, za ta dandana kudarta kan abin da suka ce ta yi wanda ya saba wa dokokin duniya.

Kasashen sun fitar da sanarwa ne ta jaddada zargin a kan Iran, bayan da Fira ministan Isra’ilar Naftali Bennett, ya ce suna da shedar cewa dadaddiyar abokar gabarsu Iran ce take da hannu a kai harin.

Mista Bennett ya nanata hakan, tare da gargadin cewa, sun san yadda suke aika wa da Iran sako ta hanyarsu.

Firaministan Isra’ila Naftali Bennett ya nuna alamun ramuwar gayya yana cewa sun san yadda suke aika wa Iran sako ta hanyarsu

Wannan hari dai shi ne na baya-bayan nan, na abin da ke kara ruruta wutar yakin da kasashen biyu – Iran da Israilar ke yi a fakaice, kasancewar ba su fito fili sun ayyana – yaki a tsakaninsu ba.

Tun watan Maris ake ta kai wa jiragen ruwan juna hari, abin da ke zamakamar ramuwar gayya. Ba kasafai ba ne ba dai ake samun salwantar rayuka a hare-haren, amma a wannan lamarin ya rutsa da rayukan dan Birtaniya da kuma dan Romania

Haka kuma Iran ta zargi Isra’ila da kai hare-hare kan cibiyoyinta na nukiliya da kuma masananta na kimiyya.

A wata sanarwa da aka fitar Lahadin nan, Sakataren Harkokin waje na Burtaniya, Dominic Raab ya ce gwamnatin kasarsa ta yi amanna Iran ta yi amfani da dan karamin jirgi maras matuki, daya ko biyu, wurin kai hari kan jirgin ruwa MV Mercer Street, yana mai cewa, hari ne da aka kai da gangan, wanda kuma karara ya saba wa dokokin duniya.

Ya kara da cewa: “Dole ne Iran ta kawo karshen wadannan hare-hare, kuma dole ne a bar jiragen ruwa su yi zirga-zirga ba tare da wani tarnaki ba.

Shi ma Sakataren Harkokin Waje na Amurka Antony Blinken ya ce gwamnatin kasarsa, ita ma tana da yakini Iran ce ta kai harin, kuma martanin da ya dace zai biyo baya.

Firaministan Isra’ila ya ce yana sa ran ganin kasashen duniya sun fito fili sun nuna wa Iran cewa ta yi babban kuskure.

Ita dai Iran ba ta amince da zargin ba, ko kadan, hasali ma, kakakin Ma’aikatarta ta Harkokin Waje Saeed Khatibzadeh, ya sheda wa manema labarai ne cewa gwamnatin Isra’ila ita ta kirkiri rashin tsaro da ta’addanci da kuma tashin hankali.

Ya ce wajibi ne Isra’ila ta daina wannan zargi maras tushe, yana mai gargadi da cewa duk tsuntsun da ya ja ruwa to dole ya yi hakuri da dukan ruwa, wanda ya ci buzu to shi zai yi aman gashi.

Ana wannan takaddama ne yayin da ake kokarin farfado da yarjejeniyar nukiliya ta duniya ta 2015 a Vienna, wadda a karkashinta za dage wa Iran takunkumin da aka sa mata bias hadin kan da ta bayar na watsi ko rage shirinta na nukiliya.

Kasashen Yammacin Duniya na zargin Iran da kokarin hada makaman kare-dangi, abin da Iran din har kullum take musantawa da cewa ita shirinta na bincike ne da kuma samar da makamashi.

More News

An Jikkata Jami’an Tsaro A Harin Da Ƴan Bindiga Su ka Kai Wa Ayarin Motocin Yahaya Bello

A jikkata wasu jami'an tsaro a wani hari da yan bindiga su ka kai kan jerin ayarin motocin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ranar...

Bala Muhammad ya zama shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP

An zaɓi gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP. Siminalayi Fabura zaɓaɓɓen gwamnan jihar Rivers shi ne mataimakin shugaban...

Za mu sake bitar mafi karancin albashi a Najeriya—Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin sake nazarin mafi karancin albashin ma’aikata domin dacewa da yanayin tattalin arzikin kasar nan. A cewarsa, akwai bukatar...

EFCC na zargin tsohuwar ministar mata a mulkin Buhari da karkatar da naira biliyan 2

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta titsiye tsohuwar ministar harkokin mata Pauline Tallen kan zargin azurta kai ta...