Buhari zai kai ziyara Birtaniya

FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai je kasar Birtaniya domin kai ziyara ta kashin kansa bayan ya kaddamar da ayyuka a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar a ranar Alhamis.

A wata sanarwa da mai ba shugaban kasar shawara kan watsa labarai Femi Adesina ya fitar, ta bayyana cewa shugaban zai kaddamar da ayyukan ci gaba a fannonin ilimi da lafiya da hanyoyi, bayan nan ne kuma zai kama hanyarsa zuwa Birtaniya.

Wannan tafiyar ta shugaban na zuwa ne kwana guda bayan ya kaddamar da wasu ayyuka a jihar Legas.

Sanarwar dai ta bayyana cewa shugaban zai dawo Najeriyar ne a ranar 5 ga watan Mayun 2019 – wato tsawon kwana 10 ke nan.

A kwanakin baya ne dai shugaban ya kai ziyara a kasashen gabas ta tsakiya inda har ya gabatar ta makala mai taken “shimfida hanyar zuba jari domin habbaka tattalin arzikin duniya a zamanance.”

Haka ma, kwanaki biyu kafin tafiyarsa zuwa kasashen gabas ta tsakiya, shugaban ya je kasar Senegal, inda ya halarci bikin rantsar da Shugaban kasar Macky Sall a karo na biyu.

A shekarar 2017 ne dai shugaban ya kwashe fiye da wata uku a kasar Birtaniya yana jinya, inda a lokacin Mataimakinsa Yemi Osinbajo ya jagoranci kasar a matsayin mukaddashin shugaba.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...