Buhari ‘ya ji takaicin’ rashin biyan Super Eagles kudadensu | BBC Hausa

'Yan wasan Super Eagles

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Madagascar ta doke Najeriya da ci 2-0 inda ta zamo ta daya a rukunin

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya yi mamakin rashin biyan ‘yan wasan Super Eagles kudadensu na alawus a gasar cin kofin Afirka ta Masar 2019.

Tun kafin wasan Najeriya da Guinea takaddama ta kaure tsakanin ‘yan wasan da Hukumar Kwallon Kafar kasar kan rashin biyansu kudaden ladan wasa kimanin dala 10,000 (Naira miliyan 3,600,000) kowanne.

Gwamnan Filato Simon Lalong ne ya gabatar da korafin ‘yan wasan ga Buhari a ganawar da suka yi a fadar shugaban kasa a Abuja bayan gwamnan ya dawo daga Masar inda ya tafi kallon wasannin Najeriya.

Buhari ya bayyanawa gwamnan takaicinsa inda ya ce ya sanya hannu a biya ‘y wasan kudadensu amma kuma ba a biya ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar NAN, ya rawaito gwamnan na cewa.

Shugaban ya ce yadda kwallon kafa ke hada kan ‘yan kasa bai kamata a yi wasa da hakkin ‘yan wasan ba.

Ya kuma yi alkawarin daukar mataki kan al’amarin da “gaggawa domin tabbatar da ganin an biya ‘yan wasan kudadensu” domin su kara samun kwarin guiwa a wasanninsu na gaba.

Najeriya dai ta sha kashi hannun Madagascar a wasan karshe na rukuni, bayan Super Eagles sun samu nasara a wasannin da suka buga da Burundi da Guinea.

Sai dai duk da haka ta samu damar kaiwa zagaye na biyu na gasar, kuma a ranar Talata ne za ta san kasar da za ta fafata da ita.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...