Shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi wata ganawar sirri da gwamnan jihar Kaduna,Malam Nasiru El-rufai da kuma na jihar Benue Samuel Ortom ranar Litinin a fadar shugaban kasa ta Aso Rock dake Abuja.
Har ya zuwa yanzu masu É—auko rahoto na dakon bayanai kan abin da ganawar ta mayar da hankali akai sai dai kamfanin Dillancin Labaran Najeriya,NAN ta ya rawaito, Ortom na cewa yaje fadar shugaban kasar ne domin sanar da shi kan halin tsaro da jiharsa take ciki.
Har ila yau shugaban kasar ya gana da gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emiefele.
Emiefele wanda a yan kwanankin nan shugaban kasa ya mikawa majalisar dattawa takardar sake neman tabbatar da shi a matsayin gwamnan babban bankin a karo na biyu ya gaisa da shugaban kasar inda ya ta ya shi murna.