Brazil ba ta gayyaci Neymar tawagar Olympic ba

Neymar

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Brazil ta bayyana ‘yan wasa 23 da za su buga mata tamaula a gasar Olympic da birnin Tokyo zai karbi bakunci a bana, amma ba Neymar a ciki.

Neymar dan kwallon Paris St Germain, mai shekara 29, baya cikin ‘yan wasa uku da aka amincewa tawaga ta dauki wadanda shekarunsu suka haura 23.

Cikin ukun da za ta je da su Tokyo domin buga mata tamula a Olympic sun hada da Dani Alves da Diego Carlos da kuma Santos.

Brazil wadda ke fatan kare zinare da ta lashe a 2016, bayan doke Jamus, ta zabi Alves ganin cewar yana daga cikin masu sa’a a wasannin tamaula da kan lashewa kungiya ko tawaga kyautuka

Cikin watan Mayu Alves ya cika shekara 38, shima yana fatan kara lashe kyautar lambar yabo a Tokyo domin karawa daga wadanda yake da su tun a baya.

Sauran ‘yan wasa 20 da aka gayyata sun kasance ‘yan kasa da shekara 23, kamar yadda doka ta tanada a gasar kwallon kafa ta Olympic.

Za a fara gasar wasannin Olympic da birnin Tokyo zai karbi bakunci daga ranar Juma’a 23 ga watan Yuli zuwa Lahadi 8 ga watan Agustan 2021.

Tun a bara ya kamata a gudanar da wasannin Olympic, amma tsoron yada cutar korona ya sa aka dage fafatawar zuwa shekarar 2021.

Tawagar Brazil da za ta buga Olympic a Tokyo.

Masu tsaron raga: Santos da kuma Brenno.

Masu tsaron baya: Dani Alves da Gabriel Menino da Guilherme Arana da Gabriel Guimaraes da Nino da kuma Diego Carlos.

Masu buga tsakiya: Douglas Luiz da Bruno Guimaraes da Gerson da Claudinho da Matheus Henrique.

Masu wasan gaba: Matheus Cunha da Malcolm da Antony da Paulinho da kuma Pedro.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...