Bosnia: Musulmai da Yahudawa na bikin shekara 200 da kulla kawance | BBC news

War of Bosnia-Herzegovina. Bombing of Sarajevo, September 1992. (Photo by Francoise De Mulder/Roger Viollet via Getty Images)

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ba a taba mantawa da wannan lamari ba, duk da yake-yaken duniya biyu da aka tafka da kuma masifar rikicin da kasar ta fuskanta cikin shekarun 1990

Musulmai da Yahudawa a kasar Bosniya na bikin cika shekara 200 da kulla kawance.

Suna shagulgulan cika shekara 200 ne a wani biki da aka yi wa lakabin Sarajevo Purim – lokacin da al’ummar Musulmi suka kubutar da rukunin wasu shugabannin Yahudawa daga gidan yarin Daular Ottoman.

Shugabannin al’umma a yanzu na cewa wannan wani misali ne da ya kamata duniya ta yi koyi.

Tun shekaru da dama da suka gabata Sarajevo ya shahara a daya daga cikin yankunan Turai da ke da mutane mafi hakurin zama da juna.

Musulmai da Yahudawa da Kiristoci daga dariku daban-daban ne suke huldodinsu cikin kwanciyar hankali da juna a babban birnin kasar na Bosniya.

Shekara 200 da ta wuce sun taba tashi tsaye suka kare makwabtansu lokacin da gwamnan Sarajevo na Daular Ottoman ya yi garkuwa da shugabannin al’ummar Yahudawa, inda dubban Musulmai suka taru suka kubutar da su.

Ba a taba mantawa da wannan lamari ba, duk da yake-yaken duniya biyu da aka tafka da kuma masifar rikicin da kasar ta fuskanta cikin shekarun 1990.

Bikin cika shekara 200 din yana jaddada kawancensu ne.

Shugaban al’ummar Yahudawan Bosniya Jakob Finci ya yi tambayar cewa, “Shin idan za su iya zama lafiya da Musulmai, me ya sa kowa ma ba zai iya yin haka ba a duniya?”

Shi ma takwaransa jagoran Musulmai Husein Kavazovic, ya ce “Karuwar kyamar da ake nunawa al’ummar Musulmai ta sa ya zama muhimmin abu su sabunta alkawarinsu na cewa za su kasance abokan makwabtaka nagari.”

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...