Bola Ahmad Tinubu : Jagoran APC ya buƙaci Buhari ya dauki matasa miliyan 50 aikin soja

An gudanar da bikin ne a jihar Kano

Asalin hoton, KSGV

Bayanan hoto,
An gudanar da bikin ne a jihar Kano

Jagoran APC a Najeriya Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya yi kira da a ɗauki matasa miliyan 50 aikin soja, domin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankunan ƙsar baki ɗaya.

Bola Tinubu ya bada wannan shawarar ne yayin taron taya shi murnar zagayowar haihuwarsa da aka saba gudanarwa duk shekara, wanda a wannan karon aka yi a jihar Kano.

Da yake nuna damuwa kan yadda yawancin matasan ƙasar ke fama da rashin aikin yi, Tinubu ya ce babban abin da yanzu ya kamata gwamnatoci su maida hankali a kai shine gina rayuwar ɗan adam, ciki kuwa har da samar wa matasa ayyukan yi.

To sai dai wannan furuci da jagoran na APC ya yi sun janyo muhawa a tsakanin wasu ‘yan kasar da kuma masu fashin baki kan al’amuran da suka shafi tsaro.

Dr Kabiru Adamu na kamafinin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a Najeriya da yankin Sahel ya ce babu yadda za a yi kasa irin Najeriya, wadda yawan al`umar bai dara na kasashe irin su China Indiya ba ta tara sojojin da suka kai miliyon biyar ba ballantana miliyon hamsin, yana jaddada cewa su ma masu yawan al`ummar ba su yi haka ba, saboda adadin ya saba wa hankali.

”Ita kanta China da tafi yawan jama’a a duniya sojojin ta miliyan biyu ne da motsi, yayin da Indiya da ke biye mata ke da sojoji miliyan daya da dubu dari hudu, don haka wannan maganar ta Tinubu ta fi gaban hankali” in ji shi

Asalin hoton, PREIDENCYTWITTER

Bayanan hoto,
Wasu dai na zargin cewa sun ɓaɓe ne da fadar shugaban ƙasa

Masanin ya ce ba mamaki ko Mista Tinubu tuntuben-harshe ya yi, ko kuma shakaru ne suka fara kama shi.

Shi kuwa masanin siyasa Malam Kabiru Sufi, na kwalejin share fagen shiga jami’a ta Kano ya ce watakila furucin na nuni ga irin zaman tsamar da ake zargin ana yi tsakanin banagaren shugaban ƙasa da jagoran

An jima ana zargin cewa ana takun-saka tsakanin Mista Tinubu da fadar gwamnatin Najeriya ganin ya yi gum da bakinsa duk kuwa da rigingimun da aka yi fama da su, ciki har zanga-zangar EndSARS da rikicin makiyaya da manoma yankin kudancin kasar.

Wasu dai na zargin cewa sun ɓaɓe ne da fadar shugaban ƙasar bayan ya fahinci ba sa goyon bayan ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, duk kuwa da cewa bai fito fili ya nuna sha`awar hakan ba.

Kodayake, a makon da ya wuce ma fadar shugaban Najeriyar ta fitar da sanarawa tana cewa babu wani saɓani tsakaninta da Mista Tinubu, bilhasali ma masu haɗa-sahu ne kawai suke kulle-kullensu.

(BBC Hausa)

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar ƙera bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...