Birtaniyya Ta Hana Daukar Likitoci ‘Yan Najeriya Aiki

Gwamnatin Britaniyya ta sanar da haramtawa hukumar kula da al’amuran ma’aikatan lafiya da masu bada kulawa a kasar daukar likitoci da ma’aikatan lafiya aiki daga Najeriya.

Gwamnatin kasar ta Birtaniyya ta sanar da wannan matakin ne a cikin wani kundin tsarin aikin lafiya da masu ayyukan jinkai cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

A yanzu, Najeriya ta shiga cikin jerin kasashen da suke fama da rashin wadatattun ma’aikatan lafiya a bisa bayyanan WHO.

Wani majinyacin harin bom din da aka kai a Maiduguri a asibiti 16, ga Oktoba 2015.
Wani majinyacin harin bom din da aka kai a Maiduguri a asibiti 16, ga Oktoba 2015.

A watan Maris ne WHO ta fitar da sunayen kasashe 55 da suke fama da kalubalen wadatattun ma’aikatan lafiya ciki, har da Najeriya.

Sabo da haka, ya kamata a baiwa kasashen Birtaniya, Najeriya da sauran kasashen da aka ayyana fifiko wajen inganta baiwa ma’aikatan lafiya horo da kuma al’amuran da suka danganci bada taimako ta yadda za a hana daukan ma’aikatan lafiya a kasashen waje.

Sakon da kundin ya kunsa shine “bisa tsarin dokar WHO” kuma kamar yadda karara dokar ta bayyana cewa za a yiwa dokar tsarin aikin kwaskwarima bayan duk shekaru goma, ya kamata a baiwa wadannan kasashen fifiko wajen baiwa ma’aikatan lafiyarsu horon aiki domin su dada samun kwarewar aiki kana a dakatar da daukan su aikia A kasashen waje.

Cibiyoyin lafiya da kuma cibiyoyin dake baiwa al’umma kulawa, cibiyoyin daukar ma’aikata da sauran masu alaka da daukar ma’aikatan lafiya masu hadin giwa su kiyaye daukar ma’aikatan lafiya daga wadannan kasashe har sai idan an samu tattaunawa ta fahimta tsakanin gwamnatocin kasashen wanda

Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo
Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo

WHO ta rubuta sunayen kasashen dake da bukatar tallafin da kariyar da jan alli. Har idan an cimma jarjejeniyy tsakanin kasar da ta haramta cibiyoyn daukar maikata, ana sanya kasar cikin wannan rukunin kasashen.

Dokar ta kuma ce, har idan ba a rubuta sunan kasar da jan alli ba to yana kasancewa a rukunin masu koren alli. Kasashen da aka yiwa haramcin daukar ma’aikata sune Kenya da Nepal kawai.

Maikatan asibiti suna lura da mara lafiya
Maikatan asibiti suna lura da mara lafiya

Idan za a iya tunawa, wani kudirin dokar haramta baiwa likitoci ‘yan Najeriya da suka samu horon aikinsu a kasar takadar shaidar kwarewar aiki har sai sun kwashe mafi karancin shekaru biyar suna aiki a kasar, yayi masarar samun karatu na biyu a majalisar wakilan kasar a ranar alkhamis din da ya gabata.

Manufar dokar itace rage yawan likitocin da suke neman barin kasar su fita aiki a kasashen waje kana a inganta ayyukan lafiya a Najeriya.

More News

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...

Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da...