Connect with us

Hausa

‘Biri ya cinye naira miliyan 7 a gidan zoo a Kano’ | BBC Hausa

Published

on

goggon biri

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Jami’an kula da gidan namun daji na zoo da ke Kano sun ce suna bincike kan wani goggon biri da ya cinye naira miliyan bakwai.

Shugaban gidan zoo din Umar Kashekobo ya ce: “‘Yan sanda na bincike kan ainihin abin da ya fau – abin da zan iya cewa kawai shi ne kudi sun bata.”

Mai magana da yawun ‘yan sandar jihar Abdullahi Kiyawa ya ce kudaden shiga gidan zoo din na kwana biyar ne suka yi batan dabo.

Ya shaida wa BBC cewa zuwa yanzu an kama mutum 10 kuma jami’ai na binciken abin da ya sa ake ajiye kudi mai yawa haka ba tare da kai su banki ba.

A farkon makon nan gidan rediyon Freedom a Kanon ya sanar da bacewar kudin.

Gidan rediyon ya yi hira da wani ma’aikacin bangaren kudi na gidan wanda ya ce goggon birin ya sulale ya shiga cikin ofishin ne ya sace kudaden tare da cinye su.

A shekarar da ta gabata ma wata ma’aikaciya a hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta Jamb reshen jihar Benue, ta ce wani maciji ya shiga ofishin ya hadiye naira miliyan 36 kudin jarabawar da aka tara.

Makonni kadan da suka gabata ita da wasu jami’an suka musanta hannu a batan kudin.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Arewa

Me ya sa gwamnatin Ganduje ke takun saka da mawakan Kannywood? | BBC Hausa

Published

on

Ganduje da Naziru da oscar

Kamun da rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta yi wa Naziru M. Ahmed ranar Laraba da yamma ya sake tado da sabuwar kura kan rikicin siyasar da yake faruwa a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC cewa sun kama mawakin ne “saboda kalaman batanci” da ya yi a cikin wasu wakokinsa.

Ya kara da cewa ana tuhumar mawakin da gudanar da dakin yin waka, wato sutudiyo, a gidansa, zargin da mawakin ya musanta.

Sai dai Malam Aminu Saira, dan uwan mawakin, ya gaya wa BBC cewa ‘yan sanda sun sanar da su cewa ‘gwamnatin jihar Kano ce ta sa aka kama shi ta hannun hukumar tace fina-finai ta jihar Kano’.

“An kama Naziru ne saboda fitar da wani kundin waka da ya yi mai suna ‘Gidan Sarauta’ da kuma ‘Sai Hakuri’. Mun yi kokari a ba mu belinsa jiya da daddare amma an ki,” in ji Saira — a lokacin Naziru yana gidan yari kafin a sako shi.

Hasalima, a cewarsa, an fitar da kundin wakar ne shekara hudu da suka gabata.

Tuni dai Naziru ya bayyana a gaban wata kotun Majistare a birnin Kano. An bada belinsa da sharuda wadanda suka hada da bayar da kudi naira dubu 500, da mika fasfo dinsa na tafiye-tafiye, da kuma gabatar da mutane uku da zasu tsaya masa, wadanda dole su kasance ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da kuma dagacin yankin da yake zaune.

Mun yi kokarin jin ta bakin shugaban hukumar tace fina-finan, Isma’ila Na’abba Afakallah, amma bai amsa kiran wayar da muka yi masa sau da dama ba. Kazalika bai yi martani kan sakon text da na WhatsApp din da muka aika masa ba.

Sai dai jaridar Daily Trust ta ambato shi yana musanta cewa siyasa ce ta sa ake cin zarafin mawakan yana mai cewa sun keta dokokin hukumar tace fina-finai ne.

‘Alaka da Sarki Sanusi da Kwankwasiyya’

Naziru shi ne Sarkin Wakar Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, mutumin da ya dade yana kai ruwa rana tsakaninsa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje lamarin da ya kai ga rarraba masarautarsa zuwa gida biyar.

Kazalika, mawakin fitaccen dan kungiyar Kwankwasiyya ne, wato bangaren siyasar jam’iyyar hamayya ta PDP da tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso ke jagoranta ne.

A 2015 dai tsohon gwamna Kwankwaso ya yi ruwa ya yi tsaki wurin ganin Gwamna Ganduje ya ci zabe – kuma sun yi nasara. Amma daga bisani sun raba gari.

Aminu Saira na ganin cewa kama kanin nasa bai rasa nasaba da siyasa, domin kuwa, a cewarsa, “idan dan uwan nasa ya yi waka ‘yan kasuwa yake sayarwa. Don haka su ya kamata a tuhuma. Kazalika kamfanin da yake buga wakar “nawa ne ba na Naziru ba, don haka idan suna da matsala da wakokin ni ya kamata su tuntuba.”

Wannan dai ba shi ne karo na farko da hukumar tace wakoki da fina-finai ta Jihar Kano ke kama jarumai da mawakan Kannywood ba.

Wasu jarumai da masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood na ganin a yanzu hukumar ta mayar da hankali ne wajen musgunawa wadanda ake jin suna adawa da gwamnati.

Kafin kamun da aka yi wa Naziru sarkin waka, hukumar tace fina-finan ta kama Sadiq Zazzabi da kuma a baya bayan nan Sunusi Oscar bisa zarge-zarge da suka hada da saba kai’dar aiki.

A takaice, hukumar ta ce ta kama Sanusi Oscar ne saboda “ya fitar da wata waka wadda ke nuna badala”, yayin da shi kuma Sadiq Zazzabi aka kama shi saboda zargin saba wa dokar da ta ce wajibi ne duk sabuwar wakar da za a fitar sai an gabatar da ita ga hukumar don tacewa da kuma samun sahalewarta.

Za mu sanya kafar wando daya da Afakallah

Sai dai jarumi kuma mai bayar da umarni, Falalu Dorayi, ya shaida wa BBC cewa kamen da aka yi wa dukkan mawakan uku na da alaka da siyasa.

Hakkin mallakar hoto
Instagram/real_dauda_kahutu_rarara

Image caption

Wasu ‘yan Kannywood sun yi zargin cewa Rarara shafaffe ne da mai shi ya sa ba a daure shi ba

“Da farko ya kamata ka sani cewa dukkan wadannan mawaka ‘yan PDP ne kuma sun yi shura wajen caccakar gwamnatin Kano ta APC. Idan har da gaske ne cewa an kama su ne domin sun saba doka, me ya sa ba a taba kama Dauda Kahutu Rarara ba? Babu wanda ba ya zagi a cikin wakarsa amma tun da dan jam’iyyar APC ne sun kasa kama shi.”

Tuni dai fitattun jarumai irin su Adam Zango da Mustafa Naburaska suka bayyana cewa sun dakatar da yin fim a jihar Kano, har sai lokacin da gwamnati ta daina cin zarafin ‘yan fim.

Kazalika, jarumai irin su Sani Danja da Ali Nuhu sun yi kira a bi a hankali kan yadda ake kama mawaka da ‘yan fim.

Su ma jaruman fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya ba a bar su a baya ba wajen sukar gwamnati kan kamun da aka yi wa mawakan Kannywood.

Fitacciyar jarumar nan Kate Henshaw ta gargadi hukumar tace fina-finan jihar Kano kan musgunawa mawaka.

Su ma masu sharhi a masana’antar Kannywood sun ce wadannan kame-kame take hakkin dan adam ne da ‘yancin fadin albarkacin baki, kuma za su iya jawo mummunar gaba a masana’antar.

Muhsin Ibrahim mai nazari ne kan fina-finan Kannywood, kuma ya shaida BBC cewa “kama mawaƙa da gwamnatin Kano take abin takaici ne ga Kannywood. Yana ƙara jawo rarrabuwar kai da gaba a tsakanin mutanen masana’antar wadda dama tuni alaƙa ta yi tsami a tsakaninsu.

Ya kara da cewa “hakan zai kashe bunƙasar masana’antar da kuma sa tsoro a zukatan mawaƙa da sauran mutane. A hankalce, ba dole ne kowa ya bi bayan gwamnati mai ci ba. Cusgunawa mawaƙa na nufin a daina adawa, wadda kuma ba zai yiwu ba.”

Sai dai ya yi kira ga mawakan da su bi doka “su kuma yi adawa mai tsafta da kuma hankali”.

Amma Falalu Dorayi ya ce idan har gwamnati ta ci gaba da amfani da hukumar tace fina-finai wurin cin zarafin ‘yan fim, to ba za su yi kasa a gwiwa wajen adawa da ita ba.

“Muna kira ga shugaban hukumar tace fina-finai ya sani cewa ya daina bari ‘yan siyasa suna amfani da shi wurin cimma burinsu. Amma idan ba haka ba, za mu sanya kafar wando daya da shi kuma za mu yi galaba a kansa kamar yadda muka yi a kan magabacinsa,” in ji Dorayi.

Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

An kai hare-hare kan matatun mai na Saudiyya da jirage BBC Hausa

Published

on

•Abqaiq matatar mai ce mafi girma a duniya

Kafofin yada labarai na gwamnatin Saudiyya na cewa an kai wasu hare-hare da jiragen sama masu sarrafa kansu a gabashin kasar.

An dai kai hare-haren ne kan wasu wurare biyu da ake sarrafawa da adana albarkatun man fetur.

Jami’an gwamnatin kasar sun ce gobara ta tashi a sanadiyyar hare-haren musamman a matatar mai ta Abqaiq – wanda ita ce irinta mafi girma a duniya – da kuma a Khurais, inda ake hako mai.

Kafofin watsa labarai na Saudiyyar sun ce an shawo kan gobarar da ke ci. Tun farko, hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda gobarar ta haska samaniya a Abqaiq.

A wasu bidiyon, ana iya jin karar harbe-harbe a bayan fage, tamkar ana gwabza fada.

Babu wanda ya san takamamai wdanda suka kai wanann harin.

Matatar mai ta Abqaiq na karkashin kulawar kamfanin mai na Saudiyya ne wato Aramco.

Abqaiq na da nisan kilomita 60 a kudu maso yammacin Dhahran a lardin gabashin Saudiyya, inda Khurais kuwa na da nisan kilomita 200 ne kudu da Abqaiq, wanda shi ne wuri na biyu a girma da Saudiyya ke hako man fetur.

Dakarun Saudiyya sun taba dakile wani hari da al Qaeda ta so ta kai a yankin a 2006. Kuma Saudiyya ta rika amfani da makaman ta na kariya wajen dakile wasu hare haren da ‘yan tawayen Houthi ke kai wa daga Yemen.

Wadanda ake ganin su ne suka kai hare-haren

An dora alhakin kai wasu hare-hare da aka kai cikin Saudiyya kan mayaka ‘yan Houthi na kasar Yemen.

A wancan karon, sun kai hari ne kan wata masana’antar samar da iskar gas a Shaybah cikin watan Mayu, har ma da wasu wuraren da ake sarrafa man fetur.

Kungiyar ta ‘yan Houthi na da alaka ta kut-dakut da kasar Iran, kuma tana neman kwace iko ne daga hannun gwamnatin Yemen wadda hadakar kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta ke mara wa baya.

Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

‘Yan Najeriya sun yi zarra a gasar karatun Kur’ni a Saudiyya | BBC Hausa

Published

on

Wadanda sukja yi nasara a gasar karatun Kur'ani ta 2019 a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto
@makkahregion

Image caption

‘Yan Najeriya uku ne suka yi zarra a gasar ta bana

Wasu ‘yan Najeriya uku Abubakar Muhammad da Amir Yunus Goro da kuma Abdulganiyyi Amin sun yi nasarar lashe kyautuka a gasar karatun Al Kur’ani ta 2019 a kasar Saudiyya a matakai daba-daban.

Gwani Idris Abubakar Muhammad daga jihar Borno ta Najeriya, ya zo na daya ne a ajin farko na izu sittin ba tare da tafsiri ba.

Wannan nasara da ya samu ta ba shi damar lashe kyautar riyal na Saudiyya 120,000 – kimanin kusan naira milyan ₦12,000,000.

Sai Amir Yunus, wanda shi kuma ya zo na uku a ajin farko na izu sittin da tafsiri, inda ya samu kyautar riyal 150.000 – sama da naira miliyan ₦14,000,000.

Abdulganiyyi Amin shi ne na ukun, wanda ya zo na uku shi ma a aji na biyu na izu sittin ba tare da tafsiri ba.

Shi kuma ya samu kyautar riyal 40,000 – kusan naira miliyan ₦4,000,000.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: