Bidiyon dukan da aka yi wa wasu ƴan mata a gidan marayu na Saudiyya ya ta da kura

Hukumomin Saudiyya sun ƙaddamar da wani bincike bayan yaɗa wasu bidiyo da aka watsa a intanet da ke nuna yadda ake dukan wasu ƴan mata a gidan marayu.

Tun da farko yaduwar jerin bidiyon na cin zarafin matan a gidan marayu na Khamis Mushayt, a yankin kudancin Asir, ya haifar da ce-ce-ku-ce sosai inda masu fafutuka a shafukan sada zumunta suka yi tur da lamarin, tare da jan hankalin hukuma ta dauki tsattsauran mataki a kan waɗanda suke da hannu a lamarin.

A cikin bidiyon da ba za a iya tabbatarwa ba, an ga yadda ƴan sanda da wasu jami’an tsaro suka kai samame a wurin.

An ga wani jami’i yana jan wata yarinya a ƙasa ta hanyar riƙe gashinta ita kuma tana ta tsala ihu, yayin da wani ɗan sanda kuma ke dukanta da bel. Sannan sauran yaran kuma ana bin su da gudu ana dukansu da sanda.

Babu tabbas kan lokacin da lamarin ya faru, amma wata mata a shafin Tuwita da ta ce ita ta gyara bidiyon, ta ce ƴan mata suna zanga-zanga ne kan cin hanci da rashin adalcin da ake musu, bayan da suka gabatar da ƙorafi amma aka ƙi sauraronsu.

Daga baya ta wallafa hotuna da ke nuna ciwukan da ta ce an ji wa yaran a garin dukan tare da zargin cewa wani babban jami’i ya yi musu barazana idan har ba a sauke bidiyon daga shafukan sada zumunta ba.

Masu fafutukar kare hakkin ƴan adam sun harzuƙa sosai bayan ɓullar bidiyon a ranar Talata da daddare, yayin da maudu’in “Khamis_Mushait_Orphans” ya fara tashe a shafukan Tuwita a Saudiyya.

Wata ƙungiyar kare hakkin ɗan adam mai cibiya a Birtaniya, ALQST, ta ce bidiyon yana da ɗaga hankali, kuma ya kamata hukumomin Saudiyya su kama masu laifin.

Kungiyar da ke fafutikar kare hakkin bil adama ta National Assembly ta yi tur da lamarin da ta kira mai muni, tare da neman samar da kariya ga ƴan mata a gidajen marayu don ba su damar ƴancinsu na rayuwa.

Karin wasu labaran da za ku so ku karanta

Gwamnan yankin Asir, a wata sanarwa ranar Laraba, ya ce ya kafa kwamiti don binciken bidiyon kuma za a miƙa sakamakonsa ga hukumomin da suka dace.

Lamarin ya zo a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan ƴancin mata a Saudiyya, inda a shekarun baya-bayan nan gwamnatin ƙasar ta ɗage haramcin tuƙin motar mata tare da sassauta dokokin muharrami yayin da kuma ta dinga kama fitattun mata masu fafutuka da aka kama a ƙoƙarinta na rufe bakin masu bore.

Wata ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Dawan, mai cibiya a Amurka, ta ruwaito a wannan makon cewa an yanke wa wata mata hukuncin ɗauri a gidan yari har na tsawon shekara 45 saboda wani saƙo da ta wallafa da ke sukar shugabannin masarautar.

Wasu takardun kotu sun nuna hukuncin da aka yanke wa Nourah bint Saeed al-Qahtani saboda amfani da intanet wajen keta darajar ƙasar da take dokoki ta hanyar amfani da shafukan sada zumunta.

Kazalika an yanke wa wata ƴar Saudiyya Salma al-Shehab, mai karatun digiri na uku a Jami’ar Leeds, kan amfani da Tuwita a farkon watan nan.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...