Asalin hoton, Zamfara Government House
Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad ya ce an samu ingantuwar matsalar tsaro a tsawon lokacin da ya jagoranci jihar fiye da yadda al’umma suka zata.
A cewarsa ‘A cikin kwana dari, sai da muka yi kusan kwana hamsin da uku ba a taba kowa ba’.
A lokacin da aka tattauna da shi cikin shirin ‘A Fada A Acika’ na BBC Hausa, gwamnan ya ce duk da cewa ya iske matsaloli da dama da ke addabar jihar, amma ya fi mayar da hankali ne a kan matsalar tsaro.
Ya bayyana tsaro a matsayin muhimmin al’amari wanda idan babu ba za a samu ci gaba ba a sauran ɓangarori.
“Idan ba ka samar wa al’umma tsaro ba, ana cikin karatu za a je a watsa makarantar.”
A lokacin da aka tambayi gwamnan cewa, amma har yanzu ana ci gaba da kai hare-hare a jihar ta Zamfara sai ya ce: “Amma ka san ko maƙiyin Allah ya san an samu sauƙi a Zamfara, ba kamar da ba”.
Ya kuma ƙara da cewa magance matsalar tsaro abu ne da zai iya daukan lokaci kafin a magance ta baki ɗaya.
Asalin hoton, Zamfara Government House
Bello Matawalle ya zama gwamnan jihar Zamfara ne bayan da kotu ta tabbatar da haramcin zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC da aka yi a jihar gabanin babban zabe na shekara ta 2019.
Matsalar tsaro a jihar Zamfara kafin wannan lokaci ta haifar da kisan mutane masu dimbin yawa da kuma raba dubban al’umma da muhallansu.
‘Wasu sun mayar da daukar makami sana’a‘
Gwamnan na jihar Zamfara ya kuma kara da cewa wasu mutane a yankin na jihar Zamfara sun mayar da kai hare-hare a matsayin sana’a.
A cewar sa talaucin da ya ke addabar al’umma ya ƙara tsananta matsalar, domin wadansu ta wannan hanya ce suke rike kansu.
“Wani ya maida abin sana’a, kafin ka raba shi da wannan abin ba karamin abu ba ne.”
Ya kuma ce jami’an tsaro suna yin iyakar bakin kokarin su wajen ganin an magance matsalar ta tsaro.
Asalin hoton, Zamfara Governmnt House
Sai dai wasu daga cikin al’ummar da suka yi tsokaci kan matsalar tsaro a lokacin tattaunawar sun bayyana cewa har yanzu akwai sauran aiki, domin kuwa ‘yan bindiga na kai hare-hare suna korar mutane daga kauyuka, haka nan wasu na ganin cewa akwai matsala game da sulhun da gwamnatin jihar ta yi da ‘yan bindiga.
Daya daga cikin wadanda suka yi tsokacin kan tsaro ya ce “Tun daga bakin Rukudawa, da Sanu, da Madobiya, da Tungar-Buzu da duka yankunan da ke wannan wurin gaskiya ba su zaune lafiya. Yanzu haka guduwa muke yi muna gudun hijira zuwa Birnin-Magaji da Birnin-Tsaba.”
Wani kuma ya ce “An ce an yi sasanci tsakanin ‘yan ta’adda da gwamnati, amma mu ba mu ga ci gaban sasancin ba, muna koke ga mai daraja gwamna idan bai sani ba yanzu ya sani, sasancin nan mu muna ganin har yanzu akwai gyara.”
Hira ta musamman da gwamnan Zamfara
Taɓarɓarewar Ilimi da aikin gwamnati
Baya ga matsalar tsaro an kuma yi wa gwamnan tambayoyi kan wasu ɓangarorin na daban.
Farida Garba ta yi wa gwamnan tambaya kan yara miliyan daya da rahotanni suka bayyana cewa ba su zuwa makaranta, inda ta ce “Ta wace hanya ce za a magance matsalar?”
Nura Kabuga ya yi magana kan inganta aikin gwamnati da yi wa ma’aikata karin albashi. Inda ya yi zargin cewa har yanzu ana naɗa ‘yan siyasa mukaman manyan daraktoci da kuma sakatarorin gudanarwa.
Sai dai a lokacin da ya amsa tambayar Nura Kabuga, gwamna Muhammad Bello ya ce gwamnatinsa na naɗa ‘yan siyasa a matsayin manyan daraktoci ne saboda a samu hanyar taimaka wa al’umma wurin kawar da talauci, sai dai ya ce dukkanin sakatarorin gudanarwa da ke jihar ma’aikatan gwamnati ne, ba nadin siyasa ba.
Ya ce gwamnatinsa tare da hadin gwiwar hukumar bayar da ilimi ta bai daya ta gina makarantu sama da dari a cikin wata biyar, sannan kuma za a gina wasu kusan guda 160 domin magance matsalar yara marasa zuwa makaranta.
‘Abubuwan da na fi bai wa muhimmanci‘
Daya daga cikin wadanda suka halarci tattaunawar mai suna Muzammil Muhammad Idris ya tambayi gwamnan kan abubuwan da gwamnatinsa ta fi bai wa muhimmanci.
Gwamnan ya zayyano su kamar haka:
A cewar sa tsaro shi ne abin da ya fi muhimmanci, daga nan sai inganta ilimi, da kuma inganta kiwon lafiya.