BBC Hausa: Kroos da Tchouameni ba za su yi wa Real wasa da Liverpool ba

Tchouameni and Kroos

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid ta sauka a Ingila domin karawa da Liverpool a wasan zagayen farko a Champions League zagayen ‘yan 16 da suka rage a gasar.

Sai dai kungiyar Sifaniya za ta buga wasan ba tare da Toni Kroos da Aurlien Tchouameni ba, amma Karim Benzema yana cikin ‘yan wasa.

Benzema, wanda ya lashe Ballon d’Or na jinyar da bai samu buga karawar da Real ta ci Osasuna 2-0 ba ranar Asabar.

Sai dai tsohon dan wasan tawagar Faransa, mai shekara 35 ya samu halartar atisayen tunkarar Liverpool da za su fafata ranar Talata.

Cikin ‘yan wasan da za su fuskanci Liverpool ba Kroos da Tchouameni, wadanda ba su samu damar buga fafatawa ba da Osasuna.

Sai dai koci, Carlo Ancelotti na fata ‘yan wasan za su murmure da wuri domin fuskantar Atletico Madrid ranar Asabar a La Liga.

Haka kuma Real za ta fafata da Barcelona a daf da karshe a Copa del Rey zagayen farko ranar 2 ga watan Maris a Santiago Bernabeu.

Real ta yi nasara a kan Liverpool da ci 1-0 a Champions League a wasan karshe a bara, inda kungiyar Sifaniya ta dauki na 14 jimilla a Stade de France.

Liverpool za ta ziyarci Santiago Bernabeu a wasa na biyu a Champions League ranar 15 ga watan Maris.

More from this stream

Recomended